Manchester United na son Rakitic, Guardiola na son tafiya hutu

Man United Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption United ta kare a mataki na shida a kakar da aka kammala

Manchester United na bukatar ta kashe kudade masu yawa idan har tana son dauko 'yan wasan baya wato Wan-Bissaka na Ingila mai shekara 21 daga kungiyar Crystal Palace da kuma Harry Maguire mai shekara 26 daga kungiyar Leicester City.

Farashinsu zai kai fan miliyan 130, wanda zai kasance mafi girma da ta taba lale wa a baya yayin cinikayyar 'yan wasa, kamar yadda Standard ta ruwaito.

Har wa yau, United ta fara tuntubar Barcelona kan dan wasanta Ivan Rakitic dan kasar Croatia mai shekara 31, kamar yadda jaridrun Spain suka ruwaito.

Sannan kuma kungiyar na son daukar dan wasan bayan Norwich City Max Aarons mai shekara 19 idan suka gaza samun Wan-Bissaka, in ji Sky Sports.

An kuma shawarci matashin dan wasan baya na Ajax Matthijs de Ligt da ya koma Manchester United inda zai samu damar buga wasanni idan ya so daga baya sai ya koma Barcelona. Sport ta ruwaito.

Sai dai jaridar Mundo Deportivo ta ruwaito dan wasan yana cewa "bai san abin da zuciyarsa ke so ba" amma zai yanke hukunci idan ya tafi hutu.

Kocin Manchester City Pep Guardiola yana tunanin tafiya hutu a karshen kakar bana idan ya samu nasaar lashe kofin Zakarun Turai na Champions League, in ji jaridar Star.

Labarai masu alaka