Najeriya za ta iya zama kamar China – Buhari

Buhari
Image caption Shugaba Buhari ya yi alkawarin hada kan 'yan kasar

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babu abin da zai hana kasar ci gaba kamar kasashen China da India ko Indonesia.

"Tun da China da India da Indonesia suka ci gaba, to babu abin da zai hana Najeriya ci gaba," a cewar shugaban, wanda aka sake zaba karo na biyu a watan Fabrerun da ya gabata.

Ya kara da cewa: "Kasashen China da Indonesia sun ci gaba karkashin tsarin mulkin mulukiya yayin da India ta kai gaci a karkashin tsarin demokuradiyya, a don haka muma babu abin da zai hana mu mu kai ga gaci".

Shugaban na magana ne a ranar bikin murnar demokuradiyya, wacce a karon farko ake tunawa da ita a ranar 12 ga watan Yuni.

An sauya ranar ne daga 29 ga watan Mayu domin tunawa da kuma rage radadin alhinin soke zaben shugaban kasa na 1993.

Shugaba Buhari ya kuma sanar da sauya sunan filin wasa na Abuja zuwa Moshood Abiola, mutumin da aka yi imanin cewa shi ne ya lashe zaben na 1993 wanda gwamnatin sojin lokacin ta soke.

Wannan sanarwa dai ita ce ta fi birge wadanda suka halarci wurin taron idan aka yi la'akari da yadda wurin ya kaure da tafi bayan da ya ayyana hakan.

Jawabin Buhari

Shugaba Buhari ya shafe dogon lokaci yana jawabi inda ya bayyana rawar da Najeriya take takawa wurin tabbatar da demokuradiyya da kuma inganta tsaro a nahiyar Afirka.

Sannan ya lissafa abubuwan da ya ce gwamnatinsa ta samar a shekaru hudun da ya yi a kan karagar mulki wadanda suka hada da:

Hakkin mallakar hoto Punch
Image caption Mayan jami'an gwamnati da na jam'iyya mai mulki su ne suka mamaye wurin taron
 • Inganta harkokin tsaro - ciki har da yaki da Boko Haram - wanda ya ce ya tabarbare a lokacin da ya hau mulki a 2015
 • Sai dai ya ce har yanzu akwai sauran aiki domin masu satar mutane da 'yan bindiga na ci gaba da addabar jama'a
 • Kowa ya san mun yi nisa a yaki da cin hanci da kuma samar da ayyukan yi
 • Gyara kuraren da gwamnatocin baya suka yi
 • Bunkasa tattalin arziki da yaki da talauci
 • Samar da ayyukan ci gaba da suka hada da gina hanyoyi

Abin da zai mayar da hankali a kai

Duk da cewa shugaban bai ayyana wani takamaiman alkawari ga 'yan kasar ba, amma ya bayyana wasu abubuwa ko fannonin rayuwa da ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hanakali a kai a wa'adin mulkinsa na biyu.

 • Dorawa kan ayyukan cigaban da ya ce gwamnatinsa ta samar a fannoni daban daban
 • Tabbatar da hadin kan kasar da kuma yi wa kowanne bangare adalci
 • Yaki da talauci - za mu iya raba mutum miliyan 100 da talauci idan aka samu kyakkyawan shugabanci
 • Inganta harkokin lafiya a matakin kananan hukumomi da gwamnatocin tsakiya
 • Tallaffawa masu kananan masana'antu
 • Gina kananan hanyoyi domin agazawa 'yan kasuwa da manoma
 • Bayar da tallafi ga masu zuba jari
 • Kammala gina hanyoyi na tsawon kilomita 2000
Hakkin mallakar hoto Punch
Image caption Manyan baki daga ciki da wajen Najeriya sun halarci bikin
Hakkin mallakar hoto Punch
Image caption Cikin wadanda suka halarta har da wasu shugabannin kasashen Afirka

Bikin ya samu halartar wasu shugabannin Afirka da suka hada da na Rwanda da Chadi da Nijar da kuma Gambia.

Haka kuma akwai manyan jami'an gwamnati ciki har da sabbin shugabannin majalisun dokoki na tarayya.

Sai dai babu daya daga cikin tsaffin shugabannin kasar da ya halarci taron. Haka kuma babu jami'an babbar jam'iyyar hamayya ta PDP.

Labarai masu alaka