'Yan Houthi sun kai hari filin jirgin saman Saudiyya

Houthi-run Al-Masirah TV posted a photograph of a missile launch Hakkin mallakar hoto Al-Masirah TV
Image caption 'Yan tawayen sun sha kai irin wannan harin roka zuwa cikin Saudiyya

A kalla fararen hula 26 ne suka samu raunuka a sanadiyyar wani harin roka da 'yan tawayen Houthi suka kai kan wani filin jirgin sama a kudu maso yammacin Saudiyya, in ji rundunar sojojin kasar.

Mata uku da kananan yara biyu na cikin wadanda suka sami raunuka a lokacin da rokar ta fada wa dakin karbar fasinjojin da suka sauka a filin jirgin sama na Abha da safiyar Laraba.

'Yan tawayen ma sun sanar da cewa sun kai harin wani makami mai linzami kan filin jrgin saman.

Saudiyya ce ke jagorantar wata hadakar kasashen Larabawa da mara wa gwamnatin Yemen a yakin da ta ke yi da 'yan tawayen Houthi a shekara hudu da suka gabata.

Rikicin ya daidaita Yemen tun watan Maris na 2015 lokacin da ya kara kazancewa.

A wancan lokacin, 'yan tawayen Houthin sun kwace yawancin yankin yammacin kasar, dalilin da ya tilastawa Shugaban kasar Abdrabbuh Mansour Hadi ya tsere zuwa kasashen waje.

Saboda damuwar cewa Iran ce ke mara wa 'yan Houthin baya da kayan yaki, Saudiyya da wasu kasashen yankin suka fara yakin mayar da Mista Hadi kan mukaminsa.

Kakakin rundunar sojojin da Saudiyyar ke jagoranta, Kanar Turki al-Maliki ya ce 'yan Houthin sun harba wata roka kan babban filin jirgin sama na Abha da karfe 2:21 na ranar Laraba (11:21 agogon GMT).

Kanar Maliki ya kuma ce wannan harin da aka kai kan filin jirgin saman na iya zama laifin yaki a karkashin dokokin kasa-da-kasa. Filin jirgin saman na da nisan kilomita 110 daga iyakar Saudiyya da Yemen.

Tashar talabijin ta Al-Masirah ta ruwaito kakakin 'yan tawayen Houthi Birgediya-Janar Yahia Sari na cewa makamin da suka harba mai linzami ne.

Ya kuma ce "Makaman kariya da Amurka ta ba Saudiyya ba su iya kare ta daga harin ba, kuma wannan matakin ya razana abokan gabarmu".

Tashar Al-Masirah ta ce wannan ne karo na biyu da 'yan Houth ke harba irin wannan rokan cikin Saudiyya.

Na farko shi ne harin da suka kai kan wata tashar samar da hasken lantarki mai amfani da makashin nukiliya da ake aikin ginawa a Abu Dhabi a 2017.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan Houthin sun ce za su ci gaba da kai hare-hare kan filayen jirgin saman Saudiyya har lokacin da ta janye dakarunta daga filin jirgin sama na Sana'a

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yakin na Yemen ya janyo mutuwar fararen hula 7,000 kuma 11,000 sun sami raunuka.

Kimanin kashi 65 cikin 100 na wadanda suka mutun sun rasa rayukansu ne a sanadiyyar harin da dakarun hadakar da Saudiyya ke jagoranta suka kai.

Dubban fararen hular kasar kuma sun mutu saboda dalilai da suka hada da rashin abinci, da cututtuka da rashin koshin lafiya.

Labarai masu alaka