Yarinya ta kashe kanta 'saboda an saki babarta' a Kano

Kano Map Taswira

Wata matashiya ta kashe kanta a jihar Kano da ke arewacin Najeriya wacce ake zargin takaicin sakin mahaifiyarta da mahaifinta ya yi ne ya sa ta aikata hakan.

Marigayiyar mai suna Halimatus Sadiyya ta mutu tana da shekara 17, kuma daliba ce a makarantar sakandare a unguwar Tudun Murtala da ke karamar hukumar Nasarawa.

Wakilin BBC a Kano Ibrahim Isa, wanda ya ziyarci gidansu marigayiyar a yayin da ake karbar gaisuwa, ya ce ya ga kungiyoyin jama'a daban-daban maza da mata na shiga da fita don yin ta'aziyya, "kuma yawanci suna cikin kaduwa".

Bayanan da ke fitowa daga bangaren iyayenta na nuna cewa takaici ne ya rufe Sadiya bayan mahaifinta ya saki mahaifiyarta, har ta gwammace ta bar duniya maimakon ta ci gaba da ganin bakin ciki.

Malam Kabiru Hamza dan sanda ne, kuma kanin mahaifin marigayiyar, ya shaida wa BBC cewa: "An samu sabani ne tsakin kaninta da kanwar mahaifinta, amma an sasanta su komai ya wuce.

"To bayan faruwar abin ne sai mahaifiyarta ta je suna mayar da maganganu ita da mahaifiyarmu, wato surukarta kenan.

To shi yayana sai ya doki wannan yaro da aka samu sabani da shi, ita kuma uwar sai ta yada magana ta ce hankali ya kwanta tun da an sa an daki yaron".

"Wannan abu dai har ya yi zafi har aka sake ta. Daga bisani manya suka shiga ciki aka sasanta amma duk da haka ta ce ba za ta zauna ba. Sai ta tattara kayanta ta tafi.

"To ita kuma Halima ita ce babbar 'yarta, kuma dama ta ce idan aka saki babarta to ko me ye ma zai iya faruwa da ita. Sai ta dauki wani sinadari irin na kamfanin shuka ta sha, daga bisani sai ta fito tana kukan ciwon ciki tana cewa a taimaka mata," in ji Kabiru Hamza.

Ya kara da cewa daga nan ne aka kai ta asibiti cikin gaggawa amma tuni rai ya yi halinsa.

Rasuwar Halimatus Sadiyya ta yi matukar tayar da hankalin iyaye da danginta, musamman ma hanyar da aka ce ta bi wajen kashe kanta.

Malama Sakina, kanwa ce ga mahaifin marigayiyar, ta kuma ce "Sadiya mutuniyar kirki ce wacce ba za a manta da ita ba."

Jihar Kano na cikin jihohin da ke fama da matsalar mutuwar aure a Najeriya.

Sai dai mahukunta da kungiyoyi masu zaman-kansu na ikirarin daukar matakai daban-daban da nufin daidaita sahun ma'aurata ta hanyar wayar da kansu a kan illar mutuwar aure, da musamman ma yadda take shafar 'ya'ya.

Amma ga alama har yanzu da sauran aiki.

Sai dai lamarin marigayiya Sadiyya, kamar yadda danginta ke cewa bai kai ya shafi dangantakarta da iyayenta ba, kasancewar suna zaman lafiya in ban da wannan karon da aka samu akasi, kamar yadda Malam Kabiru Hamza ya ce.

"Babu wata rashin jituwa tsakanin iyayenta lafiya kalau suke zaune," in ji shi.

A Najeriyar dai a kan samu mutanen da kan kashe kansu sakamakon halin takaicin da sukan samu kansu, misali sakamakon auren dole ko gorin rashin haihuwa.

Amma yadda lamarin a baya-bayan nan ke daukar sabon salo, yake kuma ritsawa da masu rangwamen shekaru ya fara tayar da hankalin al'umma.

Labarai masu alaka