Camfe-camfe kan bayar da gudunmawar jini

Person giving blood Hakkin mallakar hoto Getty Images

Akasarin mutane suna bayar da gudunmawar jini idan suna cikin koshin lafiya kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta bayyana.

Amma akwai wasu sharudda da idan ba a bi su ba za su iya dagula lamura wanda hakan zai sa a fara tunanin camfe-camfe.

Ga wasu daga cikin camfe-camfen da muka gano ba gaskiya ba ne da kuma gyara kan alakarsu da bayar da gudunmawar jini.

Marassa cin nama ba sa bayar da gudunmawar

Abin da za a duba cikin wannan lamarin shi ne sinadarin Ayon (Iron), daya daga cikin ginshikan jini ne, amma ana damuwa kan cewa jinin wadanda ba sa cin nama ba shi da sinadarin sosai.

Amma ko da kuwa mutum ba ya cin nama, muddun yana cin nau'ikan abincin da ke gina jiki, zai samu wadataccen sinadarin a cikin jininsa.

Amma kuma idan jinin mutum ba shi da sinadarin na Ayon (Iron) din sosai, bai kamata ya bayar da gudunmawar jini ba saboda tsaron lafiya.

Marassa lafiya da masu ciki da kananan yara ba sa bayar da gudunmawar jini

Wannan da gaske ne. Mutanen da suke da cutar HIV ko kuma ciwon hanta da tarin fuka da kuma sauran cututtuka irin haka da ake dauka ba sa bayar da jini.

Duk wata alama ta mura ko sanyi ko kuma mashako da tsutsar ciki kan iya sa a ki daukar jinin mutum a asibiti idan yaje bayar da gudunmawa.

Sai mutum ya warke gaba daya daga duk irin wadannan cututtuka a kalla da kwanaki 14 kafin ya iya bayar da jini.

Haka kuma idan mutum yana shan magunguna, sai ya jira ya kammala tukuna kafin ya bayar.

Ka'idoji kan shan magunguna sun sha bam-bam idan aka yi la'akari da kasashe.

Haka kuma idan mace tana da ciki, ko ba ta dade da haihuwa ba ko kuma tana shayarwa ko kuma cikinta ya zube, to lallai ya kamata ta dan dakata sai ta samu wadataccen sinadarin Ayon ( Iron) a jininta kafin ta bayar da jini.

Amma al'ada ga mata ba wata kwakkwarar hujja ba ce da za su ce ba za su bayar da jini ba.

Karancin shekarun bayar da gudunmawar jini shi ne shekara 16, amma wannan ya danganta dangane da dokokin kowace kasa.

Babu wasu takaimaiman shekaru da za a ce idan mutum ya kai ba zai iya bayar da gudunmawar jini ba amma dai wasu kasashen sun saka shekaru 60 a matsayin shekarun da idan mutum ya kai bai kamata ya bayar da gudunmawar jini ba.

Ayyuka masu hadari

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Rayuwa baki dayanta na cike da hadari, wasu daga cikin irin wadannan abubuwan kan iya dakatar da mutum daga bayar da jini.

Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewa dabi'u masu hadari da suka hada da luwadi da madigo ko kuma karuwanci kan sa mutum a dakatar da shi idan ya je bayar da kyautar jini har sai an tantance lafiyarsa sa'annan.

Haka ma amfani da kwayoyi domin nishadi ta hanyar allura kan iya jawo matsala wajen bayar da jini.

Kasashe da yawa sun haramta wa masu irin wadannan kasadar bayar da jini amma kuma wasu suna ganin hakan kamar wata hanya ce ta nuna wariya.

Jininku ba zai kare ba

Hakkin mallakar hoto Getty Images

An bayyana cewa akalla mutum baligi yana da lita biyar ta jini cikin jikinsa- ya danganta da nauyin jikinsa. A lokacin bayar da jini, jikin mutum kan yi rashin jini da ya kai 500ml.

Mutane da dama musamman masu cikakkiyar lafiya kan mayar da jinin da suka rasa cikin sa'o'i 24 zuwa 48.

A takaice dai, idan...

  • Kuna da cikakkiyar lafiya
  • Kuna da nauyin akalla kilo 50 zuwa 160
  • Kuna da tsakanin shekaru 18 zuwa 66
  • Ba ku da juna biyu ko kuma ba ku shayarwa
  • Ba ku da cutar HIV
  • Ba ku yi ayyuka masu hadari ba kasa da watanni 12

......to akwai alamun cewa kuna da cikakkiyar lafiyar da za ku bayar da gudunmawar jini.

Labarai masu alaka

Karin bayani