Sojojin Sudan sun amsa laifi kan kisan 'yan adawa

Wasu masu zanga-zanga a Sudan Hakkin mallakar hoto AFP/Getty
Image caption Sojoji sun harbe gwamman masu zanga-zangar neman mika mulki ga farar hula

A karon farko majalisar soji ta mulkin wucin-gadi a Sudan ta amince cewa ita ta bayar da umarnin tarwatsa masu zanga-zanga a kasar, wanda a yayin hakan aka harbe gwamman mutane.

Sai dai kuma ana ganin daukar alhakin ba wai yana nufin za su bayar da damar gudanar da bincike na kasa da kasa ba, mai zaman kansa.

Kakakin majalisar soji ta mulkin wucin-gadin ya amsa cewa an yi kura-kurai a yayin tarwatsa masu zaman dirshan din a wajen hedikwatar sojin kasar da ke tsakiyar babban birnin kasar ta Sudan, Khartoum.

Ya nuna nadamar ne bayan kwana goma da faruwar lamarin, sannan kuma ya ce an kama wasu daga cikin sojojin kan irin rawar da suka taka a kashe-kashen farar hular, domin yi masu tambayoyi kuma za a bayyana sakamakon binciken ranar Asabar.

Amma kuma ya kara da cewa daga yanzu ba wani gungun masu zanga-zanga da za a kara bari ya je kusa da sansanonin soji.

Kafin wadannan kalamai na kakakin sojin, masu gabatar da kara sun bayyana sabbin tuhume-tuhume da aka yi wa tsohon shugaban kusar, Omar al-Bashir, wanda aka hambarar a cikin watan Afrilu.

Bayan cajin da aka yi masa a watan da ya wuce, a kan kisan masu zanga-zanga da ke neman ganin ya sauka daga mulki, a yanzu masu gabatar da karar sun zarge shi da cin hanci da rashawa.

Yanzu dai ana shirin wani yunkuri na diflomasiyya na hadaka wanda ya kunshi Amurka da kungiyar kasashen Afirka, AU, domin samun masalaha ta siyasa da kuma tsara yadda za a mika mulki na wucin-gadi kamar yadda masu boren suka bukata ga farar hula.

Alamu dai na nuna cewa duk da irin kalaman da 'yan majalisar sojin ta mulkin wucin-gadi suka yi cewa suna da niyyar mika mulkin ga farar hula, abubuwan da suka yi a watan da ya wuce, sun nuna alamun cewa ba su da niyyar mika mulkin.