Kwace makamai ne maganin matsalar tsaro - Sanata Matori
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Sai Gwamnatin Najeriya ta kwace makamai daga farar hula - Sanata Matori

Matsalar tabarbarewar tsaro a Najeriya na ci gaba da ci wa jama'ar kasar tuwo a kwarya inda ake yawan samun hare-haren 'yan bindiga da kuma sace mutane domin neman kudin fansa musamman a arewa maso yammacin kasar.

Ko a karshen mako, hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutane akalla talatin da hudu a wani hari da aka kai kauyen Tungar Kahau da ke karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara.

Sanata Salisu Ibrahim Musa Matori, tsohon dan majalisar dattawan Najeriya ne, kuma ya shaida wa Is'haq Khalid cewa kamata ya yi gwamnatin kasar ta kwace makamai daga hannun farar hula a fadin kasar.

Latsa alamar lasifika a hoton sama domin sauraren cikakkiyar hirar:

Labarai masu alaka