Ya za ku yi idan kuka ga damisar Google a dakinku?

cat and bear Hakkin mallakar hoto Kate Bevan

Google ya fitar da wani sabon tsari da zai bai wa masu amfani da manhajar Android damar ganin dabbobi masu motsi da fitar da sauti a wani salo "kamar a zahiri" wanda a Turanci ake cewa 'Augmented Reality' (AR) ta kamarar wayarsu.

A yanzu tsarin na aiki ne kan wasu dabbobi kawai amma za a fadada shi zuwa kan wasu abubuwan nan gaba.

Na'urorin da ke da irin wannan tsarin yanzu sun hada da wasu samfurin wayoyin Huawei da Samsung da LG da OnePlus.

Haka kuma, Apple na da manhajojin da ke iya nuna tsarin Augmented Reality kuma wasu masu amfani da wayoyin iPhone na iya amfani da wannan tsarin yayin da wasu ba sa iyawa.

Hakkin mallakar hoto Richard Latto

Ya tsarin ya ke aiki?

  • Idan aka binciki sunan wata dabba a Google (hotunan wasu dabbobin ba sa aiki da tsarin, don haka sai an yi ta gwadawa - amma ana samun hotunan wasu kamar Kare da Mage da Maciji da Mikiya da Damisa
  • Idan hoton dabbar yana cikin tsarin, a cikin wani akwati a kusa da hoton dabbar za a rubuta sako kamar haka: "hadu da maciji mai girman na gaske"
  • A cikin akwatin akwai maballi da ke cewa "a gani a nau'in tiridi (3D)"
  • Sai a danna maballin sannan a zabi inda aka rubuta "kalla a cikin dakinka"
  • Daga nan tsarin zai bude kamara sannan ya bayar da umarnin a haska ta a kasa
Hakkin mallakar hoto Dan Condon

Tsarin AR dai wata hanya ce ta hada hotuna da zahiri kuma an kirkiri fasahar ne tun kafin kirkirar wayoyin hannu na zamani amma ci gaban da wayoyin suka samu ya kara fito da fasahar musamman a wasannin da ake bugawa a kan wayoyin na hannu kamar wasan kwamfiyuta na Pokeman Go.

Manhajar shagon siyar da kayan daki na IKEA na bai wa kwastomomi damar jera kayan daki a gidajensu ta hanyar amfani da tsarin AR don ganin yadda kayan za su yi a gidan kafin su siya.

Wata masaniya a fagen tsaron intanet, Lisa Forte ta yi gargadin cewa dole ne masu kirkirar shafukan intanet da masu amfani da manhajojin AR su yi taka tsan-tsan kan tsaro.

"Shi ma AR ana iya yi masa kutse kamar shafukan intanet da manhajoji," a cewarta.

Ta ce "Abin dubawa shi ne a karfafa zubinsa da yadda ake fitar da shi."

Labarai masu alaka