'Yan matan Afirka Ta Kudu sun isa Masar a jirgin da suka kera

L-R: Agnes Keamogetswe Seemela and Megan Werner
Image caption Megan (ta hannun dama) na daga cikin matukan jirgin sai kuma Agnes (ta hannun hagu) wacce take cikin mataimaka

Wani jirgin sama da wasu 'yan mata suka kera a Afirka Ta Kudu ya sauka lafiya a Masar mako uku bayan tashinsa daga birnin Cape Town.

Wasu dalibai 20 daga bangarori daban-daban na kasar ne suka kera jirgin mai wajen zaman mutum hudu.

'Yan matan sun tsaya a Namibiya da Malawi da Ethiopia da Zanzibar da Tanzaniya da kuma Uganda a yayin tafiyar mai tsawon kilomita 12,000.

Matukiyar jirgin Megan Werner 'yar shekara 17 wacce ita ce ta kirkiri shirin na U-Dream Global ta ce: "Ta ji dadi matuka da suka cimma wannan buri.

"Na ji dadin yadda aka girmama ni a duk inda muka tsaya a nahiyar sabodasauyin da muka kawo.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Jirgin da matasa suka kera a Afirka Ta Kudu ya isa Alkahira

"Babban dalilin kera jirgin shi ne don a nuna wa Afirka cewa komai zai iya yiwuwa idan dai ka sa wa ranka hakan," kamar yadda ta ce.

Wani karamin jirgin mai wajen zaman mutum hudu da kwararru suka tuka ne ya yi wa na matasan rakiya a bulaguron, wadanda suka dinga yi wa sauran matasa bayani na kara kwarin gwiwa a yayin da suke rakiyar.

Matasan sun kera jirgin ne cikin mako uku, daga na'u'rorin da aka suka samu a kamfanin kera jirage na Afirka Ta Kudu. An yi amfani da dubban wasu kananan bangarori wajen hada jirgin.

Mahaifin Meghan Des Werner wanda matukin jirgin fasinja ne, ya ce ya kan dauki mutum awa 3,000 kafin ya kera jirgi mai zaman mutum hudu.

"Idan ka raba awannin ga yara 20 da za su yi aikin cikin sa ido za a iya kammala shi cikin mako uku.

Kwararru ne suka duba injinan da kyau, amma yaran ne suka kera jikin jirgin," in ji shi.

"Idan na kalli jirgin na kan yi alfahari da kaina, na kuma yi ta mamakin wai mu muka yi wannan aikin,' in ji Megan.

"Ina jin kamar cewa wannan jaririna ne. Ina son sa," a cewar Agmes Keamogetswe Seemela, mai shekara 15 daga garin Munsiville a gundumar Gauteng.

"Yana keta hazo lafiya lau kuma kallonsa na da ban sha'awa," kamar yadda ta fada a tashin farko da ya yi daga birnin Johannesburg zuwa Cape Town, gabannin ya fara bulaguro a hukumance zuwa wata kasar.

Agnes Keamogetswe Seemela,
BBC
At first people in my community were shocked - they didn't believe me when I told them I helped build a plane... But now they're actually very proud of me"
Agnes Keamogetswe Seemela
Student, 15, from Munsiville township

"Ina daga cikin wadanda suka yi aikin kera jikin jirgin da kuma fuka-fukansa."

Matashiyar 'yar shekara 15 ta ce tana fatan aikinta zai kara wa wasu guiwa.

Image caption Yana daukar mutum awa 3,000 kafin ya kera jirgi mai zaman mutum hudu

"Da farko al'ummar yankina sun kadu sosai - ba su yarda da ni ba lokacin da na fada musu cewa da taimakona aka kera wani jirgi wanda zai tashi daga Cape Town zuwa Alkahira."

""Amma a yanzu kuwa alfahari suke da ni."

Karin labaran da za ku so ku karanta

Megan ta ce balaguron ya hadu da irin nasa kalubalen.

Ba su samu man fetur ba a Addis Ababa babban birnin Ethiopia.

"A yayin da a karshe muka samu kuwa, jirgin da ke mana rakiya ya fara tsiyayar da mai don haka ba su iya karasawa da mu ba - don haka da ni da Driaan van den Heever mai taimaka min muka ci gaba," a cewar Megan.

"Mun nuna damuwa wajen wucewa ta Sudan saboda rashin zaman lafiyar da ke faruwa a kasar."

Megan 'yar shekara 17 ce ta fara aiki, sauran kuma da suka taimaka mata a aikin na U-Dream Global an zabo su ne daga mutum 1,000 da suka so shiga aikin.

Tana daya daga cikin mutum shida a kungiyarsu da ta samu lasisin tuka jirgin sama, kuma su shida din za su dinga sauyi wajen tuka jirgin ne a tsakanin su, kuma an zana taswirar Afirka a jikin fuka-fukan jirgin da kuma tamburan wadanda suka dauki nauyi.

"Samun lasisin tukin jirgi daidai yake da kammala digiri - kuma yin hakan a lokacin da nake tsaka da jarabawar makarantata ba abu ne mai sauki ba," a cewar Megan, wacce ta yi jarabawarta ta kammala makaranta a watan Oktoba, yayin kuma da a hannu guda take shirye-shiryen kera jirgin.

Megan Werner
BBC
It's just awesome to see how inspired people are by what we've done"
Megan Werner, 17
Pilot and U-Dream Global founder

Sai dai lasisin nasu ya zo da kalubale saboda ba a ba su izinin yin sama sosai ba sai dai su dinga tafiya ta yadda za su dinga hango kasa, kuma an hana su shiga gajimare.

Zangon karshe na tafiyar daga Addis Ababa zuwa Alkahira ta Aswan, ya fiddo da ainihin hazakar yaran.

Ni da Driaan van den Heever mun yi tafiya mu kadai har tsawon sa'a 10 ba tare da jirgin da ke mana rakiya ba, don haka matasa biyu ne kawai mu kadan mu ba mataimaki," a cewar Megan

Isa Masar

Matukan biyu sun gamu da wani cikas a na'urar jirgin sa'a guda kafin su shiga sararin samaniyar Masar.

Don haka sai suka yanke shawarar sauka a daya daga cikin kananan filayen jirgi mafi kusa a Alkahira maimakon babban filin jirgin saman kamar yadda aka shirya da afari.

"Hakan ya jawo 'yar karamar matsala amma dai an yi hakan ne saboda gudun gamuwa da wata babbar matsalar," in ji Des Werner.

Megan ta ce: "A yyain da muka sauka a Masar hukumomi sun so kama mu, suka kwace mana fasfuna da lasisinmu amma bayan sa'a hudu aka warware komai kuma muka samu karin mai muka ci gaba da tafiya zuwa Aswan.

"Daga Aswan muka wuce Alkahira kuma gaskiya na ji matukar dadi da muka sauka a nan."

Labarai masu alaka