Nigeria suicide blast 'kills 30' in Borno
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kalli bidiyon harin da Boko Haram ta kai gidan kallo

Masu aikin ceto a Najeriya sun ce a kalla mutum 30 ne suka mutu bayan da aka kai wasu hare-haren kunar bakin-wake a wani gidan kallo a arewa maso gabashin kasar.

An kuma raunata wasu mutum 40 a harin, wanda aka kai a garin Konduga da ke jihar Borno.

Maharan sun tayar da bama-baman da suke dauke da su ne a wani gida da mutane suka taru domin kallon talbijin.

Wani ganau ya shaida wa BBC cewa wata 'yar kunar bakin wake ce ta fara tayar da bam a rumfar mai shayi da misalin karfe 8.30 na dare.

Akwai hotuna masu tayar da hankali a wannan bidiyon.

Labarai masu alaka