Amincewa da allurar riga-kafi na raguwa a duniya

vaccine Hakkin mallakar hoto Getty Images

Yadda jama'a suke ci gaba da kin amincewa da sahihancin alluran riga-kafi na jawo koma-baya a yaki da cutuka masu saurin kisa, wadanda za a iya kare su, kamar yadda masana suka yi gargadi.

Wani babban nazari da aka yi kan yadda jama'a suke kallon sahihancin riga-kafi ya nuna cewa mutane da dama suna dari-dari da ita.

Binciken da cibiyar Wellcome Trust ta yi ya tattara bayanai daga mutum 140,000 daga kasa 140.

Wannan na zuwa ne yayin da hukumar lafiya ta duniya WHO ta zayyana dari-darin mutane ga allurar riga-kafi a matsayin daya daga cikin matsaloli 10 da suke kawo wa lafiyar duniya barazana.

Wani binkicen na duniya baki daya ya gano yadda mutane masu yawan gaske suke kyamar allurar riga-kafin.

Yayin da aka tambaye su ko alluran sahihai ne?:

  • Kashi 79% (takwas cikin goma) sun amsa da cewa "ga shi nan dai" ko "kwarai kuwa".
  • Kashi 7% sun amsa da "ga shi nan dai" ko "sam ba sahihai ba ne".
  • Kashi 14% ba su bayyana ra'ayoyinsu ba ko kuma sun ce "ban sani ba" kawai.

Da aka tambaye su ko riga-kafi na aiki?:

  • Kashi 84% sun yarda ta hanyar amsawa da "ga shi nan dai" ko kuma "kwarai kuwa".
  • Kashi 5% ba su yarda ba, ta hanyar amsawa da "kwarai kuwa" ko kuma "ga shi nan dai".
  • Kashi 12% ba su amsa ba ko kuma suka ce "ban sani ba".

Me yasa aka damu?

Akwai hujjoji masu yawsan gaske da suka tabbatar cewa riga-kafi ita ce babbar hanyar kariya daga cutuka masu hatsari, kamar kyanda.

Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Cutar kyanda tana da hadari sosai

Riga-kafi tana bai wa biliyoyin mutane kariya a fadin duniya.

An rabu da wata cuta har abada, kamar bakon-dauro sannan kuma muna taimakawa wajen kawo karshen wasu, kamar Shan-inna.

Sai dai wasu cutukan masu wuyar sha'ani kamar kyanda suna sake dawowa, kuma masana sun ce kyamar da mutane ke nuna wa riga-kafi ce bisa camfe-camfe da labaran kanzon-kurege ke jawo hakan.

Dokta Ann Lindstrand kwararriyar likita kan riga-kafi a Hukumar Lafiya (WHO) ta ce matsalolin da ake ciki yanzu masu girma ne sosai.

"Kyamar riga-kafi a wasu wurare na taimakawa wajen kawo nakasu ga ci gaban da aka samu a duniya game da cutukan da ake iya mnagancewa ta hanyar riga-kafi.

"Muna ganin dawowar cutukan a matsayin ci baya kuma abu ne da ba za mu amince da shi ba."

Kyanda ta dawo

kasashen da suka kusa kawo karshen cutar kyanda sun yi ta fama da annoba iri-iri.

Bayanai sun nuna karuwar cutuka a kusan kowane yanki na duniya, inda aka samu karin kashi 30% a 2017 sama da yadda aka samu a 2016.

Rashin yin riga-kafi yana kawo barazanar kamuwa da cutuka ga daidaiku da kuma daukacin jama'ar gari.

Idan aka yi wa mutane isassu, riga-kafin zai taimaka wajen hana yaduwar cuta ga al'umma - abin da masana ke kira "garkuwa ga a'umma" ko kuma "herd immunity" a turance.

Imran Khan na cibiyar Wellcome Trust ya ce: "Akwai damuwa a halin yanzu a kan kyanda. In dai har ba a cim ma kashi 95% na riga-kafinta ba to za a iya samun annoba kuma abin da yake faruwa kenan a yanzu."

Me ke jawo rashin yardar?

Iyalai wadanda ke zaune a garuruwan da ke da tattalin arziki mai kyau su ne ba su fiye dari-dari da sahihancin allurar riga-kafi ba sosai.

A kasar Faransa daya daga cikin kasashen Turai da suke fama da annobar kyanda, duk mutum daya a cikin uku bai yarda da sahihancin riga-kafi ba.

Wannan shi ne kaso mafi girma da za a iya samu a kowacce kasa a duniya.

Ana sa ran yiwuwar cewa 'yan Faransa na cikin wadanda za su ki yarda da sahihancin riga-kafin (kashi 19%), sannan kuma su ki amincewa cewa tana da amfani ga kananan yara (kashi 10%).

Yanzu haka gwamnatin kasar ta kara allurar riga-kafi takwas a kan uku da suka wajabta a yi wa kananan yara.

A makwabciyar Faransa kuma wato Italiya, inda kashi 76% suka amince da sahihancin riga-kafi, an kafa dokar hana yaran da ba ayi wa riga-kafin ba shiga makaranta ko kuma cin tarar iyayensu.

Burtaniya har yanzu ba ta bi sahu ba, amma sakataren lafiya Matt Hancock ya ce "akwai yiwuwar" bullo da allurar riga-kafi ta wajibi ga jama'a.

Amurka tana fuskantar irin tata annobar kyandar, wadda ita ce mafi grima da ta barke a kasar cikin shekaru, inda aka tabbatar da mutum 980 sun kamu da cutar a jiha 26 cikin shekarar 2019 kadai.

A arewacin Amurka da kudanci da kuma arewacin Turai, kashi 70% ne suka amince da sahihancin riga-kafi.

Sakamakon ya yi kasa sosai da na yammacin Turai (kashi 59%) da kuma gabashin Turai (kashi 50%).

A kasar Ukraine, inda aka ruwaito mafi yawan kamuwa da kyanda a nahiyar Turai a bara (53,218), kashi 50% ne kawai na mutane suka amince cewa riga-kafi tana aiki.

Kashi 46% ne suke da irin wannan ra'ayi a kasar Belarus, 49% a kasar Moldova, sai kuma 62% a Rasha.

Labaran yin nasara

Mafi yawan al'ummar da ke zaune a wuraren da tattalin arzikinsu ba shi da yalwa sun aminta cewa allurar riga-kafi tana da sahihanci.

Yankin kudancin Asiya shi ne kan gaba, inda kashi 95% na jama'a suka amince, gabashin Afirka ke biye masu da kashi 92%.

Kasashen Bangladesh da Rwanda sun cim ma kusan kashi 100% wajen amincewa da sahihancin riga-kafi, sannan sun cim ma kashi mai yawa na yin allurar duk da kalubalen da suke fuskanta na kai alluran ga mutane.

Kuna bukatar shafin intanet mai karfi don kallon wannan bayanin.

Rwanda a matsayinta na kasa mai tasowa ita ce farko da ta bai wa 'yan mata damar yin riga-kafin HPV wadda ke ba da kariya daga kansar mahaifa.

Mista Khan ya ce: "Hakan ya nuna irin abin da za a iya cimmawa idan aka hada karfi wuri guda wajen yin riga-kafi".

Me ya sa mutane suke da shakku?

Hakkin mallakar hoto Getty Images

A nazarin da aka yi, mutanen da suka yarda da binciken kimiyya da likitoci da ma'aikatan jinya na da saukin kai wajen amincewa da sahihancin riga-kafi.

Amma akasin haka ake samu a bangaren mutanen da suke ci gaba da neman sani game da aikace-aikacen masana kimiyya da ma'aikatan kula da lafiya.

Rahoton Wellcome bai bayyana duka dalilan da suke sa wasu nuna shakku kan riga-kafi ba, amma masu nazari sun ce akwai wasu karin dalilai.

Wasu na ganin yin kasa gwiwa shi ma wani dalili ne - idan aka ce cutar ta daina yaduwa, wasu sukan yi sako-sako wajen shan riga-kafinta.

Dukkan magunguna ciki har da alluran riga-kafi sukan iya jawo wasu 'yan matsaloli. Amma ana gwada riga-kafi don tabbatar da sahihancinsu da amfaninsu.

Intanet za ta iya zama wata kafa da ake yada wasu bayanai wadanda wasu lokuta ba gaskiya ba ne.

A kasar Japan, jama'a na nuna damuwa game da riga-kafin cutar HPV kuma ana danganta ta da cutukan kwakwalwa, wanda masana suke ganin hakan ya shafi yadda mutane suka aminta da allurar riga-kafin.

Haka zalika, a Faransa akwai ce-ce-ku-ce kan riga-kafin wata matsananciyar mura - inda ake zargin gwamnati da kawo adadin riga-kafi mai yawa da batun da ake cewa an samar da magungunan ne cikin sauri kuma za su iya zama marasa sahihanci.

A Burtaniya ana ci gaba da samun labarai marasa sahihanci game da cutar MMR da cutar galahanga.

Dokta Lindstrand ya ce: "Babban abin da za a yi don kawar da shakku da damuwar da wasu ke nunawa game da riga-kafi shi ne bai wa ma'aikatan lafiya cikakken horo kuma su kasance cikin shirin ba da riga-kafi bisa dogaro da sahihan binciken kimiyya."

Ya ci gaba da cewa "kuma su iya bayar da amsoshi ga damuwar da wasu iyaye da al'umma ke da ita kan allurar riga-kafi."

Becky Dale da Christine Jeavans ne suka hada wannan makala; sai Debie Loizou da Scott Jarvisda kuma Katia Artsenkova wadanda suka shirya da kuma tsarawa.

Labarai masu alaka