Ko ana iya warkewa daga cutar sikila?

Sickle Cell Anemia Hakkin mallakar hoto Getty Images

An ware ko wane 19 ga watan Yunin kowace shekara don wayar da kan mutane kan cutar sikila ko amosanin jini da hanyoyin magance ta.

Amosanin jini, cuta ce da ake gado daga kwayoyin halittar iyaye, inda suke haduwa su fito ba dai-dai ba, a jikin dan da suka haifa.

kwayar halittar na fitowa da siffar lauje maimakon a kewaye kamar yadda ya dace.

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, rikirkicewar kwayoyin halittar na janyo daskarewar jini a kananan jijiyoyi a cikin jikin mutum, wanda hakan ke jinkirta wucewar jini da iskar oxygen da aka harba daga wani bangare na jiki zuwa wani.

Daskarewar jinin na janyo matsanancin radadi a baya da kirji da hannuwa da kafafuwa.

Najeriya da daya daga cikin kasashen duniya da aka fi samun wannan cutar musamman ma a arewacin kasar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

A cewar Farfesa Aisha Indo Mamman wata kwararriyar likita kan cututtukan da suka shafi jini a asibitin koyarwa na Jami'ar Ahmadu Bello Zaria , ana haifar jarirai dubu 150 da cutar, a kowace shekara.

Masu fama da cutar na yawan gajiya, sannan su kan nuna alamun jikkata ko rashin kuzari. Haka kuma idanuwansu da fatarsu kan sauya zuwa kalar ruwan kwai.

Cutar sikila na da alamomi da dama wadanda suka hada da rashin jini da ciwon jiki mai tsanani wanda ka iya janwo matsaloli kamar jiri da ciwon kirji da bugun zuciya da ciwon koda da dai sauransu.

Haka kuma gabobi na lalacewa dalilin wannna cuta sannan tana sa rashin girman jiki da yawan samun raunuka musamman a kafa.

A kasahe kamar kamaru da Jamhuriyar Congo da Gabon da Ghana da Najeriya, yawan afkuwar cutar yana kai wa kashi 20 cikin dari zuwa kashi 30 cikin dari.

Bayanai kan cutar sikila

  • Cuta ce da take shafar miliyoyin mutane a fadin duniya.
  • Yawanci yaran da ke fama da cutar na mutuwa kafin su kai shekara 5, sau da yawa saboda rashin jini ko kamuwa da cututtuka.
  • Ba a daukar ta sai dai a yi gadon ta.
  • Rashin shan ruwa sosai, sanyin gari, yawan motsa jiki da hayakin taba na iya tayar da ciwon.
  • Ana iya gujewa kamuwa da ita idan mace da namiji suka yi gwaji kafin su yi aure.

Ko yaya masu cutar suke ji?

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wata mai fama da cutar, Aisha Saleh ta yi wa BBC bayani kan yadda take ji idan ciwon ya tashi inda ta ce misalta radadin ciwon sikila ba zai misaltu ba, sai dai ayi kwatanta.

"Radadi ne a cikin kasusuwanmu, misali kafa ko hannu ko baya. Idan a kafa ne ciwon ya tashi sai ka ji kamar ana sara kafar ko ana raba ta biyu. Radadi ne mai wahalar fassarawa." a cewar Aisha.

Ta kuma ce tana fuskantar kalubale da dama musamman a bangaren karatu dalilin cutar sikilan.

Ta ce ciwon ya kan tashi a lokuttan jarabawa wanda har ya kan ja ta gaza zana jarabawar.

"Sai dai ina samun taimako daga wajen iyaye na da 'yan uwana maza da mata." a cewarta.

Ko ana warkewa daga cutar sikila?

Farfesa Aisha Indo Mamman ta ce har yanzu mutane na da karancin sanin girman cutar sikila.

Ta ce mutane sun dogara da camfi da danganta cutar kan aljannu ko maita.

Sai dai ta ce ba a warkewa daga wannan cutar ta sikila har abada, illa dai a samu sauki ko kuma a gujewa kamuwa da ita ta hanyar yin gwajin kwayoyin halitta kafin ayi aure.

"Wadanda suka ce sun warke sau da yawa sun dauki wani mataki ne na dashe bargo, a bisa fahimtar kimiyya."

Ta ce akan dauki bargon dan uwa ko iyaye ko wani makusancin mai fama da cutar sai a dasa masa, kuma daga nan idan aka yi nasara an rabu da cutar kenan.

Sai dai ta ce bayan dashen, mai fama da cutar ne kawia zai samu kariya daga amosanin jinin amma za su iya haifar 'ya'ya masu dauke da cutar.

Labarai masu alaka