Amsar tambayoyinku kan Hamadar Sahara

sahara

Wannan makala ce da ta amsa tambayoyin da masu sauraro suka aiko kan Hamadar Sahara. Mun yi bincike tare da jin ta bakin masana kan yankin da kuma wasu mutane da suka taba keta wannan hamada mai matukar girma.

Gabatarwa

Hamadar Sahara ita ce waje na uku mafi girma a duniya da mutane ba sa rayuwa a cikinsa, baya ga Antarctica da kuma Arctic. Sai dai ita Sahara ita ce waje mafi tsananin zafi a ban kasa, yayin da Antarctica da kuma Arctic kuwa suka kasance masu tsananin sanyi.

Girmanta ya kai nisan kilomita miliyan 9.4, kusan kashi daya bisa na uku na girman nahiyar Afirka, wato kenan kusan girman kasar Amurka da ta hada da Alaska da Hawaii.

Sahara ta dauki kusan kashi 30 cikin dari na dukkanin kasashen da ke Afirka. Kuma Sahara tana tsakiya ne a Afirka, kuma wuri ne da ke samun karancin ruwa.

BBC Hausa ta yi nazari ta hanyar tattaunawa da Masana ilimin yanayin kasa da kuma wadanda suka taba rayuwa da kuma ratsa Sahara, wadanda kuma suka yi kokarin amsa wasu tambayoyi da kuka aiko mana.

Hamadar Sahara
BBC
Muhimman bayanai kan Sahara

Yanki mafi tsananin zafi a duniya

  • Shekarun samuwartaMiliyan 100

  • Yawan kasashen da Sahara ta ratsa11

  • Girmanta a kilomitaMiliyan 9.4

  • Ma'aunin zafi na celsius47-50

Bayani: Farfesa Maharazu Yusuf Bebeji BUK

Asalin Sahara- Tambayar da mafi yawan masu sauraro suka aiko kenan amma ba su bayyana sunayensu ba

Asalin sunan Sahara ya samo asali ne daga harshen Larabci wato Sahra. Sahara ta kunshi mafi yawancin yankin arewacin Afirka da ke kan iyaka da yankin Sahel da kuma kasashen kudu da Sahara.

Kasashen Sahara sun hada da Aljeriya da Chadi da Masar da Libiya da Mali da Sudan da Tunisiya da Murtaniya da Nijar da kuma kasar Yammacin Sahara.

Wani masanin yanayin kasa Farfesa Maharazu Yusuf Bebeji na Jami'ar Bayero, Kano, ya ce bincike ya nuna cewa a da can shekaru aru-aru wannan yankin ba Hamada ba ce.

Ya ce wasu masu bincike sun samu wasu abubuwa da suke nuna cewa da can ita Sahara wuri ne da ke da damshi da koguna, amma samuwar yawaitar mutane a Afirka ne ya sa ruwa ya janye a wajen.

"Masana sun ce wannan ya faru ne fiye da shekara miliyan 100," in ji shi.

Ya ce masu bincike sun ce an samu kwale-kwale a sahara sannan an hako manya-manyan halittu kamar Dinasours da aka tsinto a Sahara, wanda ke nuna a can shekaru miliyoyin da suka wuce babu Sahara.

Farfesa Maharazu ya ce "Kuma Dinasour ba ya rayuwa sai wuri mai dausayi, kuma an same shi ne a yankin Agadez."

Bayanan hoto,

Yawanci gine-ginen kasa ne a yankunan daji na Sahara

Shin asalin Sahara, teku ce ta kafe?

Masanin ya ce Sahara ba teku ba ce ta kafe, domin sahara da muke da ita tana da tudu, kuma ya fi girman Najeriya wanda ke nuna cewa ba teku ba ne.

Akwai wani bangare wanda ya yi kasa da ake zaton cewa an samu tafkuna kamar Tafkin Chadi da ake tunanin sun ajiye ruwa.

Sai dai ya ce faruwarta, shi ne wurin da ke samun karancin ruwa.

"Wuri ne da iska ke tashi, ba a samun ruwan sama, sai gefenta ne ake samun sau daya tak a shekara. Wani lokaci a wata daya tak."

Amma masanin ya ce akwai lokacin da take da dausayi, kuma kamar yadda inda ba Sahara ba yake da dausayi akwai kuma lokacin da yanayin yake komawa na Sahara.

Shin tun asali akwai Sahara

Farfesan ya ce da can akwai Sahara, shekaru aru-aru tun kafin zuwan mutane.

"Shi dan adam ba a dade da samunsa ba a duniya" in ji masanin.

Ya ce kamar wasu garuruwan arewacin Najeriya, a shekaru aru-aru can baya Sahara ne.

Bincike ya nuna cewa daga baya ne yankin ya samu daga Sahara kamar yadda ake gurgusar da teku.

Hamadar Sahara
BBC
Kasashen da Sahara ta ratsa sosai

A kasashen nahiyar Afirka

  • 30%Girman yankin da Sahara ta mamaye

  • 95%Yawan Hamadar da ke Masar

  • 60%Yawan Hamadar da ke Aljeriya

  • 60%Yawan Hamadar da ke Nijar

Bayani: Farfesa Maharazu Yusuf Bebeji BUK

Shin Hamadar Sahara da kasashe nawa ta hada iyaka? Sannan yankin wacce kasa ne ya fi yawa?

Wadannan tambayoyi ne da muka samu daga dumbin mutane wadanda ba su bayyana sunayensu ba.

Ilimin yanayin kasa ya nuna cewa yankin Sahara ya yi iyaka da Tekun Atlantika daga yamma, da Kogin Maliya daga gabas, da Bahar Rum daga arewa sannan daga kudu ta yi iyaka da yankunan da ke da ciyayi amma ba bishiyoyi da yawa wato Sahel Sabana.

Wannan kasurgumin waje ya ratsa kasashe 11 na Afirka da suka hada da Aljeriya da Chadi da Masar da Libiya da Mali da Mauritaniya da Moroko da Nijar da Yammacin Sahara da Sudan da kuma Tunisiya.

Kuma daga cikinsu an bayyana cewa, kasar Masar ce ta fi yawan Sahara. Wato ita ce ta fi yawan girman Hamadar Sahara.

"Kashi 95 na Masar kusan Hamada ce, sai Aljeriya da kuma Nijar, wacce kashi 60 cikin 100 na kasar hamada ce." in ji Farfesa Maharazu.

Wadanne irin halittu da kuma tsirrai ke iya rayuwa a Hamada?

Wannan ma wata tambaya ce daga masu sauraro kusan shida.

Masana sun ce akwai halittu da ake gani a Hamada, wadanda ake ganin Allah Ya ba su kariya da za su iya rayuwa ba tare da ruwa ba.

Halittun suna da abin da za su iya ajiye ruwa, irinsu Gawo da Kafto wadanda za su iya zama tsawon lokaci ba tare da sun damu da ruwa ba.

A bangaren tsirrai akwai Dabino da ke da saiwa mai zurfi, ana samunsa ne a Hamada.

A bangaren dabbobi, akwai Rakumi wanda ake kira "Jirgin Hamada" da kan dauki kwanaki kamar mako daya ko kwana 10 ba tare da ya sha ruwa ba.

Bayanan hoto,

Ana yawan ganin rakumi wanda ake kira "Jirgin Hamada" da kan dauki kwanaki kamar mako daya ko kwana 10 ba tare da ya sha ruwa ba

Akwai kadangaru, da suke juriyar wahala, da za su iya daukar lokaci ba su nemi ruwa ba. Masana sun ce dangin kadangare da macizai za su iya jure wa karancin ruwa a hamada.

Farfesa Maharazu ya ce duk da cewa akwai wurare masu zurfi da za a iya samun ruwa a Sahara, amma halittun suna da wata halitta da Ubangiji ke kare su da zafin rana na Hamada.

Ya ce kamar yadda ake samun halittun ruwa, haka akwai halittun da ba za su iya rayuwa ba sai a wannan yanayi na Sahara. "Haka Allah Ya yi su."

Wani mutum dan kasar Nijar Abu Ila, da ya taba ratsa Sahara don zuwa Libiya ya ce ya ga tsuntsaye nau'i uku, amma bai ga tsirrai ko bishiyoyi ko gini ba.

Yanayin Sahara

Hamada tana da nau'i biyu, tana da karancin ruwa da kuma zafi. Farfesa Maharazu ya ce a lokacin rana, zafi a Sahara yakan kai ma'aunin celcius 47 zuwa 50.

Da dare kuma yanayin zai koma na sanyi, inda ma'aunin zai sauka ya dawo zuwa 15.

Ya ce halittun duk da ke rayuwa, Allah zai ba su juriyar zafi da kuma sanyin Hamada.

Bayanan hoto,

Dubban 'yan ci-rani ne ke tafiya Turai daga Afirka inda su kan bi ta Agadez kuma suna tafiyar kwana 40 a Sahara

Samun ruwan sama a Sahara

Abu Ila ya ce a kwanakin da suka yi suna tafiya "an yi ruwan sama jefi-jefi."

Masana sun kasa Hamadar Sahara kashi biyu - akwai Aric inda ake samun ruwan sama, wadanda za su iya yin noma.

Akwai kuma inda ba a samun ruwa, da ake kira Hypa Aric a Turance, kamar yankin Arlit zuwa Aljeriya, inda ake iya shafe shekara ba a yi ruwa ba.

Farfesa Maharazu ya ce akwai wani wuri a yankin Masar da aka ce an yi shekara sama da 40 ba a yi ruwa ba. Haka kuma ya ce a wuraren kudancin Agadez ana iya shuka saboda sukan samu ruwa.

Sai dai Abu Ila ya ce a tafiyar da ya yi a cikin Sahara bai ga ko da tsiro daya da ke nuna alamar ana iya shuka a wurin ba."

Abin da ke kawo sanyi da zafi?

Masanin yanayi Farfesa Maharazu ya ce yawancin makamashi da muke samu daga hasken rana ne. Kuma Hamada babu bishiyoyi, sai rairayi kuma a haka rana ta kan zo ta fadi.

Ya ce ba kamar yankin da ba Hamada ba inda itatuwa da bishiyoyi ke rike zafin da rana ta buga, amma a Hamada babu.

Dalilin da ya sa Sahara ke yin sanyi

Farfesa ya ce gajimare ya kan rike zafin da duniya ta dumama da shi daga hasken rana, amma Hamada tun da babu wannan gajemaren, to a bude sama take.

"Idan tururin ya bugi kasa nan da nan sai ya huce ya yi sama sai wuri ya yi sanyi," in ji shi.

Ana samun ruwan sha a Sahara?Masu sauraro sun aiko da wannan tambayar

Abu Ila ya ce a tafiyar da suka yi cikin Sahara dai da guzurin ruwan shansu suka tafi, kuma rijiya biyu kawai suka gani a cikin Sahara.

"Rijiyoyin kuwa su ne wacce ake cewa metal wacce take a jikin gini kuma ba ruwa a cikinta, sai kuma Ashugur ita kuma akwai ruwa a cikinta," in ji Abu Ila.

Bayanan hoto,

Masana sun ce an hako manya-manyan halittu kamar Dinasours da aka tsinto a Sahara a can baya

Ta yaya Hamada ke kwararowa?

Masu bincke sun tabbatar da cewa lallai Hamada tana gurgusowa, saboda sauyin yanayi. Yawan ruwan da ake samu ya ragu, wanda hakan ke nuna gurgusowar Hamada.

Al'umma ta yawaita, an mayar da wurare wurin noma da kiyo, wanda ke haifar da kwararowarta.

Nijar daya daga cikin kasashen da suka fi fuskantar barazanar kwararorwar Hamada, ta fi daukar matakan kariya.

An bullo da wani tsari na sassaben zamani, inda ake koyawa manoma yadda ake sassabe ba tare da kwalkwale komi ba, sai dai a yi sama-sama domin dakile kwararowar hamada.

Ya zurfin yashin hamada?

Masana sun ce akwai Hamada mai tsakuwa da duwatsu, akwai kuma mai kasa.

Kuma a cewar Farfesa Maharazu, Hamada mai tsakuwa tana da zurfi, amma ya danganta da yawan kasar da iska ta tara.

Ya ce yawanci iska ce take tara kasa a Sahara. Kuma yawanci zurfin yakan kai mita 10 zuwa mita 20.

"Mun yi wani bincike a arewacin Karamar Hukumar Yusufari ta jihar Yoben Najeriya, akwai wadda za ka samu ta kai zurfin mita 50 zuwa 100," in ji masanin.

Bayanan hoto,

garin Arawan kenan da ke arewacin Timbuktu na Mali kafin Sahara ta gurgusa ta rufe wajen a shekarar 2002

Akwai arzikin da ake samu a Sahara?

Masana sun ce akwai arziki sosai a yankin Hamadar Sahara a Afirka.

Kuma masanan sun ce rashin ruwa ba zai hana samun arziki ba ko da kura da iska sun ruguza ko sun lullube duwatsu tsawon shekaru.

Amma ba zai hana a samu ma'adinai ba, domin an samu man fetir a Nijar da Gas.

Akwai kuma zinari da ake hako wa a yankin Agadez da kuma arzikin Uranium.

Akwai kuma ma'aidanai da yawa a yankin Aljeriya da Nijar da Masar.