Kim Jong-un ya karbi wasikar da Trump ya aika ma sa

Shugaba Kim Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Kim Jong-un a lokacin da ya ke karanta wasikar da Trump ya aika masa

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya karbi wata wasika da Shugaba Donald Trump na Amurka ya aika ma sa.

Kamfanin dillancin labarai na KCNA ya ce Mista Kim ya bayyana wasikar da mai armashi, tare da son sanin muhimmin batun da ke cikinta.

Mista Kim ya yabawa Shugaba Trump, inda ya kira shi da jajirtacce, sai dai babu wani cikakken bayani da aka yi game da abin da wasikar ta kunsa.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya tabbatar da aika wannan wasika a wani sako da fadar White House ta aika ma sa.

Mai magana da yawun fadar Sara Sanders ta ce tabbas Shugaba Trump ya aikawa takwaransa na Koriya ta Arewa wasika kuma shugabannin biyu na ci gaba da tattaunawa.

A farkon wannan watan ne Mista Trump ya bayyana cewa Kim Jong-un ya aika masa wasika mai dadin karantawa.

Sai dai ba a bayyana lokaci ko ta hanyar da Trump ya aika wasikar shi zuwa Koriya ta Arewa ba.

A watan Fabrairu dai tattaunawa tsakanin shugabannin biyu a kasar Vietnam ba ta yi armashi ba.

Ana ganin wasikar ita ce matakin farko na ci gaban da aka samu tsakanin kasashen biyu tun bayan taron watan Fabrairun.

Amurka ta kafe kan dole Koriya ta Arewa ta kawo karshen shirinta na makamin nukiliya, ya yin da Arewar ta bukaci a sassauta mata takunkumi tukunna kafin ta dauki wani mataki.

Ko a watannin da suka gabata shugaba Trump na yawan yabon shugaba Kim.

A farkon watannan ya shaidawa manema labarai cewa Koriya ta Arewa za ta samu gagarumin ci gaba karkashin jagorancin Mista Kim.

Harwayau a watan Mayu da ya wuce, lokacin taron kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 da aka yi a kasar Japan, Mista Trump ya ce Kim Jong-un ya na da kaifin basira kuma ya na sa ran abubuwa masu amfani za su samu daga kasar.

Labarai masu alaka