Shekara 27 a fim: Magoya baya na taya Shah Rukh Khan murna

Shah Rukh Khan Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shah Rukh Khan na da miliyoyin magoya baya da ke bibiyarsa a shafukan sada zumunta

A ranar Talata ne fitaccen jarumin fina-finan India Shah Rukh Khan ya cika shekara 27 da fara yin fim.

Jim kadan bayan fara fitowarsa a fim, Shah Rukh Khan ya fara nuna bajinta, inda a yanzu ake masa lakabi da "sarkin soyayya" saboda kwarewar da ya yi a fina-finan soyayya.

Yana daga cikin 'yan wasan da suka fi samun lambobin yabo a tarihin masana'antar, wacce aka fi sani da Bollywood.

Tuni magoya bayansa suka fara amfani da maudu'in #27GoldenYearsOfSRK (Nasarorin Shah Rukh Khan a shekaru 27) a shafukan sada zumunta domin taya shi murna.

"Hakika na amince cewa ci gaban da aka samu a Bollywood ya samu ne kawai saboda shigowar Shah Rukh Khan a shekarun 1990".

"Sama da shekara 100 ana yin fina-finan Bollywood, amma mun yi matukar sa'a da muka zo a lokacin da @iamsrk yake jan hankalin zukatan miliyoyin magoya baya kamar ni da ku".

"Ya kamata kowa ya fahimci yadda mutumin da ba kowa ba ya zama abin koyi wanda duniya ke alfahari da shi. Akwai jarumai da dama a Bollywood amma babu wanda zai iya hada kafada da shi. Ko mai rintsi zan ci gaba da kaunar wannan mutum har karshen rayuwata".

Jarumin, wanda Musulmi ne, yana da farin jini a ciki da wajen kasar India. Yana kuma da miliyoyin magoya baya da ke bibiyarsa a shafukan sada zumunta.

Labarai masu alaka