CP Wakili yayi karin magana akan yaki da kwayoyi a Najeriya
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gwagwarmayar da na sha a yaki da 'yan kwaya - Singham

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Tsohon kwamishinan 'yan sandan jihohin Katsina da Kano ya ce ba karamin fadi tashi ya yi ba a yaki da shan miyagun kwayoyi lokacin da yake kan aikinsa.

Singham, kamar yadda ake kiransa ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa albarkacin ranar yaki da shan miyagun kwayoyi ta duniya ranar 26 ga watan Yuni.

Daga cikin matsalolin da ya bayyana da ke kawo cikas a aikin har da rashin isassun ma'aikata da kuma kayan aiki.

Ya kara da cewa duk da dai bai samu nasara 100 bisa 100 wajen dakile shan miyagun kwayoyi kamar yadda ya yi buri ba, to ya yi nasa kokarin kafin lokacin ritayarsa, sannan akwai lokutan da yake shiga tasku musamman idan ya ga matasa da mata a wannan hali.

Ga dai bidiyon yadda hirar ta kasance.

Daukar bidiyo da tace shi: Fatima Othman

Karin labaran da za ku so ku karanta

Labarai masu alaka