Trump ya gayyaci Kim Jong-Un tattaunawa

AFP Hakkin mallakar hoto AFP

Shugaba Amurka Donald Trump ya kawar da yuwuwar zaman ganawarsa ke-ke-da-ke-ke da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong Un a yayin ziyararsa zuwa yankin Koriya.

A wani sakon Twitter da ya fitar da sassafe daga wurin taron manyan kasashe 20 mafiya karfin tattalin arziki a duniya , wato G20 da ake yi a birnin Osaka na Japan, Mista Trump, ya mika goron gayyata ne kawai, ga Mista Kim, cewa idan har takwaran nasa na Koriya ta Arewa ya ga rubutun sakon, to zai hadu da shi ne kawai a yankin iyakar kasashen Koriyar biyu, ya yi hannu da shi, ya ce masa barka, yaya dai?

Daman ba wannan ne farau ba, domin ko da ganawa ta biyu ta shugabannin biyu a Vietnam can baya a watan fabrairu, ta watse ne ba tare da wata yarjejeniya ba, to amma tun a sannan sun ci gaba da musayar wasiku, wasikar da a lokacin daga baya Mista Trump ya bayyana kyakkyawa.

Tun daga sannan ake sa ran ganin hada ganawarsu ta uku, to amma wannan goron gayyata na Mista Trump ga Kim Jong Un, ya kawar ga tsammanin zamansu ke-ke-da-ke-ke illa dai kawai su hadu a yankin iyakar Koriya ta Kudu da ta Arewar, inda ba a ayyukan soji, su sha hannu kawai, kowa ya yi gaba, ya nufi inda ya fito.

Shugaban na Amurka zai ziyarci Koriya ta Kudu ne bayan taron kolin na G 20 a Japan, inda zai sauka a Seoul babban birnin Koriya ta Kudun, a ranar Asabar , a rangadin kwana biyu da zai yi a kasar da nufin ceto batun raba Koriya ta Arewa da makaman nukiliya.

Shi dai Mista Truymp ya sha nanata cewa dole ne Koriya ta Arewa ta wargaza makamanta na nukiliya kafin a cire mata takunkumin tattalin arzikin da aka sanya mata.

To amma a maimakon hakan, tun bayan ganawar shugabannin biyu a birnin Hanoi, Koriya ta Arewar sai ma kara gwajin makamai masu linzami take yi.

Ko a makon da ya wuce ya aika wa da Shugaban na Koriya ta Arewa wasika, wadda Mista Kim ya yaba da kalaman da ta kunsa.

A martanin da Koriyar ta mayar game da gayyatar ta Mista Trump, Koriya ta Arewa ta hannun mataimaki na farko na ministan harkokin wajenta Choe Son Hui, ta ce sun ga sakon na Twitter, kuma yana da kyau, amma ba su same shi a hukumance ba.

Labarai masu alaka