Zanga-zangar kin jinin yi wa mata fyade a Coci
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kalli yadda aka yi zanga-zanga kan 'fyade' a Coci

An gudanar da zanga-zangar kin jinin yi wa mata fyade da ake zargin wani fasto da yi wa mai dakin fitaccen mawaki Tim Dakolo, Bisola Dakolo.

Masu fafutuka sun yi dandazo a sassan birnin Abuja da na Legas domin yin Alla-wadai da fyaden da fasto-fasto da malamai ke yi a wurin ibada.

Sai dai Pastor Biodun Fatoyinbo a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a, ya ce sam bai taba yi wa wata mace fyade ba, inda ya yi barazanar kai Bisola gaban kuliya.

Ya kuma danganta ikrarin da wani yunkurin bata sunansa da na cocin.

Labarai masu alaka