Aladu na cikin hatsari

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Cutar murar aladu wacce ta kashe sama da aladu miliyan daya a China na ci gaba da yaduwa.

Sabbin alkaluma da wani sashe na majalisar dinkin duniya mai sa ido kan barkewar wannan cutar ya fito ya bayyana cewa an kara samun wasu aladu guda biyar masu dauke da wannan cuta makonni biyu da suka wuce.

Dukkan aladu biyar din da suka kamu da wannan cuta a kananan gonaki suke da ke kudancin Guizhou da kuma yammacin lardin Qinghai.

Wannan ne karo na 144 da cutar ke barkewa tun bayan farar barkewar cutar a kasar a bara.

Hukumar da ke kula da abinci da noma ta majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa a kalla aladu 1,133,000 ne aka yanka domin gudun wannan cuta.

Alkaluma daga watan Mayun da ya gabata sun nuna cewa yawan aladun da aka yanka a watan Mayun kawai sun kai 107,000.

Wannan cutar dai ta murar aladu har yanzu ba a samu maganinta ba kuma babu riga kafinta a kasa.

Cutar tana kashe kusan duk aladun da suka kamu da cutar.

Labarai masu alaka