Ba mu ce dole jihohi su gina wa Fulani Ruga ba - Buhari

London, Hakkin mallakar hoto Getty Images

Gwamantin Najeriya ta bakin mai magana da yawun Shugaban kasar, Malam Garba Shehu ta ce ba bu wata jihar da ta yi wa dole ta samar da Rugage domin killace dabbobin makiyaya.

A wata sanarwa da ya fitar, Garba Shehu ya ce "Ruga na nufin wani wuri da za a tsugunar da makiyaya da masu kiwon dabbobi."

Ya kara da cewa "ba wai Fulani makiyaya ne kawai za su ci gajiyar Rugar ba, duk wani mai sana'ar dabbobi zai amfana."

Rugar za ta kasance tana da makarantu da asibitoci da tituna da kasuwanni da dai sauran abubuwan da za su taimaka wajen inganta rayuwar dabbobinsu.

Sanarwar ta kara da cewa "gwamnati ba ta da niyyar kwacewa mutane filayensu ko kuma ta tursasa su yin abin da ba sa so."

Me jihohin ke fadi?

Wasu gwamnonin jihohin kasar sun gargadi gwamnatin tarayya da ka da ta kuskura ta kafa Ruga a jihohin nasu.

A ranar Talata ne dai gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya ce gina Ruga a Benue "tamkar cin fuska ne ga al'ummar jihar saboda haka ba ma goyon bayan al'amarin."

Gwamna Ortom ya yi wannan bayani ne jim kadan bayan ma'aikatan gwamnatin tarayya daga ma'aikatar Aikin Gona inda suka je da motocin tantan domin share filayen da za a gina Rugar.

Gwamnati ta ce jihohi 12 ne suka nemi su shiga shirin gwaji na Ruga.

Labarai masu alaka