Buhari ya kori shugaban hukumar inshorar lafiya

Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Najeriya NHIS Usman Yusuf Hakkin mallakar hoto Concise News]
Image caption Farfesa Usman Yusuf ya musanta zarge-zargen da ake masa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da korar babban sakataren hukumar Inshorar lafiya ta kasar wanda ya sha fama da dambarwa.

An tura Farfesa Usman Yusuf hutun dole ne a watan Oktoban bara, bayan majalisar gudanarwar hukumar ta dakatar da shi.

Daraktar yada labarai a ma'aikatar lafiyar Najeriya, Boade Akinola ta cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, ta ce korarsa ta zo ne bayan shawarar da kwamitin binciken da aka kafa don gano sanadin rikicin da ya dabaibaye hukumar, ya bayar.

Tun farko a shekara ta 2017 ne tsohon Ministan Lafiyan kasar, Farfesa Isaac Adewole ya dakatar da Farfesa Yusuf bisa zargin aikata ba daidai ba, da kuma tafka almundahana da dukiyar al'umma.

Sai dai kwararren likitan ya sha musanta wadannan zarge-zarge, yana mai cewa masu adawa da auye-sayen da ya bullo da su ne suke yakarsa.

An nada Mohammed Sambo domin ya maye gurbinsa.

Sai dai tamkar abin nan da Hausawa ke cewa abin da ya ci doma, to ba ya barin awai, ita ma majalisar gudanarwar hukumar da ta ba da shawarar a kori babban sakataren, Shugaba Buhari ya amince da rusa ta.

Hakkin mallakar hoto NHIS
Image caption A yanzu an nada Mohammed Sambo domin ya shugabanci hukumar

Korar Farfesa a yanzu, wanda ya shafe tsawon wata 10 yana hutun dole tamkar sauya shawara ce daga wurin Shugaba Buhari wanda ya dawo da shi aiki lokacin da tsohon minista Adewole ya dakatar shi a watan Yulin 2017.

A shekarar 2017 ne dai Majalisar Wakilan kasar ta nemi a mayar da Farfesa Usman Yusuf kan mukaminsa.

Kwamitin lafiya na Majalisar ya nuna cewa matakin dakatar da shi tamkar wani bi-ta-da-kulli ne kan bayanan da babban sakataren ya bayar a wani zaman sauraron jama'a da kwamitin ya yi.

Yayin zaman cikin watan Yunin 2017, ya zargi manyan dillalan inshorar lafiya da karbar makudan kudade ba tare da mutane na amfana da shirin ba, ya kuma yi ikirarin cewa an cusa sunayen bogi na mutane sama da 23,000 wadanda ake amfani da su domin fitar da kudade.

Wasu na ganin wannan ki-ki-kakar da aka samu ta yi illa ga harkar samar da insorar lafiya a kasar, tare da zargin Shuguba Buhari da jan kafa wurin daukar mataki.