Me ya sa ake sauya tunanin 'ya'yan Musulmi a China?

  • Daga John Sudworth
  • BBC News, Xinjiang
Missing in China; some of the family portraits handed to us in Turkey by Uighur parents looking for information about their children back home in Xinjiang

Wani sabon bincike ya nuna cewa da gangan China take raba 'ya'yan Musulmai da iyayensu da addininsu da kuma yarensu a yankin yamma mai nisa na Xinjiang.

A yayin da ake tsare da dubban mutane a manyan sansanoni, a lokaci guda kuma ana wani gangami na neman gina makarantun kwana.

Ta hanyar wasu bayanai da aka samu a wajen mutane da hirarrakin da aka yi da iyalai da ke kasashen ketare, BBC ta tattaro wasu kwararan hujjoji game da abin da ke faruwa da yara a yankin.

Ajiyayyun bayanai sun nuna cewa a gari guda kawai, fiye da yara 400 ne suka rasa dukkan iyayensu sakamakon tsare iyayen da aka yi ko dai a sansanoni ko kuma a gidan yari.

Ana gudanar da bincike don gano ko yaran na bukatar kulawar hukumomi.

Baya ga kokarin sauya al'adu da dabi'un mutanen Xinjiang manya, hujjoji na nuna cewa akwai wani yunkuri na yanke alakar yara da tushensu.

Bayanan hoto,

Sansanin kula da yara na Kindness Kindergarten, kamar sauran ire-irensa yana da tsaro sosai

Tsauraran matakan tsaro da aka sanya a Xinjiang, inda ake bibiyar 'yan jarida awa 24 ya sa da wuya a samu shaidu a can. Amma za a iya samu a kasar Turkiyya.

A wani dogon daki a Istanbul, gomman mutane ne ke kan layi domin bayar da labaran da ke ci musu tuwo a kwarya, inda da dama daga cikinsu suke nuna hotunan kananan yara da suka yi batan-dabo a Xinjiang.

Wata uwa ta ce: "Ban san wane ne yake kula da su ba," tana mai nuna hoton 'ya'yanta kanana mata guda uku , ta kara da cewa, "ba wani bayani dangane da su."

Ita ma wata uwa wadda ke dauke da hoto da ke nuna 'ya'yanta maza uku da mace daya, cikin kuka ta ce, "na ji an ce an kai su gidan marayu."

A hirarraki da aka yi da iyaye da 'yan uwa 60, sun bayar da bayanai dangane da batan 'ya'yansu kimanin 100 a Xinjiang.

Bayanan hoto,

Mahaifan na guduwa zuwa Turkiyya

Dukkanninsu 'yan kabilar Uighur ne, wata kabila mai yawan Musulmai da ke yankin Xinjiang na China da ke da alakar harshe da kasar Turkiyya tun tale-tale. Dubban 'yan kabilar ta Uighur sun je Turkiyya ne ko dai domin kasuwanci ko karatu ko kuma domin guje wa dokar kayyade iyali da kuma kuntata wa Musulmai da ake yi.

To sai dai a shekaru uku da suka gabata sun samu kansu a yanayi mai tsanani lokacin da China ta fara tsare dubban 'yan kabilar da wasu kananan kabilu a sansanoni.

Hukumomi a China sun ce ana ilmantar da 'yan kabilar ta Uighur din ne a 'cibiyoyin koyar da sana'a domin raba su da tsananin ra'ayin addini.

To sai dai shaidu sun nuna cewa ana tsare da dama daga cikin mutanen saboda suna bayyana akidar addinin da suke bi ne ta hanyar yin sallah ko kuma yin lullubi ko kuma yin alaka da kasashen waje kamar Turkiyya.

Ga 'yan kabilar ta Uighur, komawa Xianjing tamkar shiga kangin wahala ne. Yanzu haka mutanen da ke Xinjiang ba sa iya yin waya da 'yan uwansu da ke waje saboda akwai hadari idan aka kama mutum.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan kabilar Uighur na fama da kuntatawa bisa zargin akidar zarmiya

Wani uba da aka kama mai dakinsa aka tsare a Xinjiang ya ce yana fargabar wasu daga cikin 'ya'yansa guda takwas ka iya kasancewa a irin wannan sansanin da ke karkashin kulawar gwamnatin China.

"Ina tsammanin an kai su sansanonin da ake ajiye yara," in ji shi.

Wani sabon bincike da BBC ta dauki nauyi ya yi karin haske kan hakikanin abun da ke faruwa da wadannan dubban yaran da ma wasu daban.

Dr Adrian Zenz wani mai nazari ne dan kasar Jamus da ya yi suna wajen fallasa yadda kasar China ke tsare matasan Musulmi na Xinjiang kuma ya samu takardun da ke nuna yadda Chinar ke fadada makarantu a wani shiri da ba a taba yin irinsa ba a baya.

An fadada makarantu da gina sabbin dakunan kwana, bayan hakan ya nuna irin yadda Chinar take bai wa shirin tsugunar da yara a sansanoni cikakkiyar kulawa.

Alamu kuma na nuna shirin Chinar na kan 'yan kabila daya ne kawai.

Bayanan hoto,

Ana kebe kananan yaran da ba sa tare da mahaifansu a wata makarantar kananan yara, Sunshine Kindergarten

A shekara daya kacal wato 2017 yawan yaran da aka shigar makarantar wasa a Xinjiang ya karu da fiye da rabin miliyan. Kuma yara 'yan kabilar Uighur da sauran tsirarun kabilun Musulmi ne kashi 90 cikin dari na yawan yaran.

Hakan ne ya sa, sanya yara a makaranta a yankin na Xinjiang ya zarce adadin da gwamnati ta sanya nesa ba kusa ba.

A kudancin Xinjiang kawai, gwamnati ta kashe tsabar kudi har dala biliyan 1.2 wajen gina makarantun kananan yara.

Nazarin da Mr Zenz ya yi ya nuna karin gine-ginen da aka samu har da dakunan kwana.

Bayanan hoto,

Wata makarantar yara a yankin Xinhe mai cin yara 700 inda kuma kashi 80 cikin dari na 'yan makarantar 'yan kabilar Uighur ne

Sai dai da yake magana da BBC, Xu Guixiang, wani babban jami'in gwamnati da ke aiki a sashen yada farfagandar yankin na Xinjiang, ya ki yarda da cewa gwamnati na son killace kananan yara ne sakamakon rashin mahaifa.

"Idan har za a ce an kai dukkan iyalai zuwa makarantar koyon sana'a to wadannan iyalan suna da babbar matsala ke nan," in ji shi, yana mai dariya. "Ban taba ganin inda ake haka ba." Ya ce

To sai dai watakila babban abin da binciken Mr Zenz ya nuna shi ne shaidar da ke bayyana yadda ake kai kananan yara masu yawa zuwa makarantun kwana.

Da alama an boye wasu takardun bayanai masu mahimmanci na gwamnati daga intanet ta hanyar yin amfani da wasu kalmomin maimakon makarantun koyar da sana'a.

Mun tambayi wasu jami'ai dangane da makomar yaran da ake kangewa a sansanoni.

Wata jami'a ta shaida mana cewa " suna makarantun kwana," inda muke "sama musu wurin zama da abinci da sutura… kuma an fada mana daga sama cewa dole ne mu kula da su sosai."

Bayanan hoto,

Dubban yaran yankin Xinjiang na kabilar Uighur ba sa tare da mahaifansu

A Xinjiang, nazarin ya nuna cewa dukkanin yaran na makarantun da aka sanya wa tsauraran matakan tsaro da kangewa . Mafi yawancin makarantun suna da na'urorin kula da inda mutum yake da kuma wayoyin lantarki masu jan mutum da aka zagaye ginin da su guda 10,000.

A farkon 2017 ne dai aka bullo da wannan tsari lokacin da aka tsare mutane masu yawa.

Mr Zenz ya ce: "Ina tsammanin cewa shaidun da ke nuna dabarun tsare iyaye da yara a wuri daban-daban alamu ne da ke nuna yadda gwamnatin Xinjiang ke kokarin samar da wasu jama'a daban a nan gaba da ba su da alaka da asalinsu ko kuma addinin iyayensu ko yarensu."

Ya kara da cewa: "Na yi imani cewa shaidun na nuna wani abu da muke kira kokarin shafe wata al'umma daga bayan kasa."