AFCON: Yadda aka kori mai kambu, aka yi waje da mai masauki

'Yan wasan Najeriya na murna Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Super Eagles ta ci kwallaye ta hannun Odian Ighalo da Alex Iwobi

Za a iya cewa ko a duniyar namun daji a kan samu yanayin da mikiya ka iya surar zaki wanda ake yi wa kirari da Sarkin dawa, duk da cewa zaki na da karfi da masifa.

Ke nan nasarar da tawagar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya ta samu a kan tawagar Kamaru da ake kira da Indomitable Lions ba abu ne na mamaki ba.

Da alama fargabar da 'yan Najeriya suka nuna tun farkon fitowar jadawalin gasar wanda ya nuna alamun haduwar kasashen biyu duk da cewa rukunin kowacce daban, ta sa 'yan Najeriyar zama cikin shiri da ya kai su ga korar mai kambun gasar gida.

Kamaru wadda ita ce mai rike da kambu ta dauki kofin gasar sau biyar, inda ita kuma Najeriya ta dauka sau uku.

Yadda wasa ya kasance

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Najeriya za ta kara ne da wanda ya yi nasara tsakanin Masar ko Afirka Ta Kudu

Da farko dai dan wasan Najeriya, Odion Ighalo ya fara jefa kwallo a ragar Kamaru a minti 19 na farkon wasa, a wani bugun tazara da Najeriyar ta samu.

To sai dai minti 20 bayan cin da Najeriya ta yi, sai aka samu yanayin da dan wasan Kamarun nan mai basira, Christian Bassogog ya harba kwallo zuwa harabar Najeriya, inda shi kuma Stephane Bahoken ya zura ta a raga.

Mintuna uku bayan yin kunnen doki, sai Indomitable Lions suka kara zura wa Super Eagles kwallo ta biyu ta hannun Clinton Njie.

Jim kadan bayan komawa daga hutun rabin lokaci dan wasan Najeriya, Odion Ighalo ya farke wa Najeriya, inda sakamako ya kasance 2-2.

Bayan nan ne dan wasan tsakiya na Arsenal, Alex Iwobi ya jefa kwallo ta uku a ragar Kamaru.

Waiwaye

Kamaru ta kai wannan mataki ne bayan da ta tashi canjaras da Benin a rukunin F, inda ta zo ta biyu da maki biyar bayan Ghana.

Ita kuwa Najeriya ta kasance ta biyu anata rukunin ne bayan da ta sha kaye a hannun Madagascar da ci 2-0.

Duka Najeriya da Kamaru sun fuskanci matsaloli wurin biyan 'yan wasa alawus-alawus da kuma shirye-shiryen zuwa gasar.

Tawagar kwallon kafa ta Najeria ta samu maki uku a wasan farko na rukuni na biyu, bayan da ta doke Burundi 1-0.

Super Eagles ta zama ta farko da ta kai zagayen gaba a gasar cin Kofin Kasashen Afirka da ake yi a kasar Masar, bayan yin nasara a kan Guinea da ci daya mai ban haushi.

Za a iya cewa Najeriya ta samu nasarar kai wa zagaye na biyu da maki shida.

Ita kuma Kamaru ta kai zagayen na gaba ne da maki biyar wanda ya yi dai-dai da na Ghana wadda ta jagoranci rukunin.

Yadda South Afirka ta yi waje da Egypt mai masaukin baki

Image caption Thembinkosi Lorch ya zura kwallo daya mai ban haushi a ragar Egypt

Tawagar Bafana-Bafana ta yi ci ri tuta bayan da ta yi waje rod da mai masaukin baki da ci daya mai ban haushi.

A minti na 85 ne dai dan wasan tawagar Afirka ta Kudu, Thembinkosi Lorch ne ya yi kukan kura ya jefa kwallo daya mai ban haushi a ragar Egypt.

Dan wasan gaba na Liverpool, Mohammed Salah ya hadu da simatsin wasa a yammacin Asabar din inda ya zubar da harba wata kwallo sama.

Da ma dai kafin wasan, kocin Bafana-Bafana, Stuart Baxter ya fadi cewa za su kunyata mai masaukin bakin wato Egypt.

Kuma da ganin irin salon wasan da suka taka tun lokacin da aka busa usul din fara wasa, alamu sun nuna komai zai iya faruwa.

Yanzu haka Afirka ta Kudu za ta kara da Najeriya ne a wasan dab da na kusa da karshe ranar Laraba.

Labarai masu alaka