Za a fara kama masu lasisin bindiga

Bindiga Hakkin mallakar hoto Getty Images

Babban Sufeton 'yan sandan Kenya ya ce za a fara kama dubban mutanen da suka mallaki bindiga a kasar, wadanda kuma suka ki bin sabbin dokokin da aka bullo da su na gabatar da kansu ga hukuma.

Kasar ta bullo da tsrain ne domin sake nazarin cancantar wadanda ya kamata su samu izinin mallakar bindiga, domin magance matsalar da ke ta'azzara ta aikata miyagun laifuka.

Sufeto Janar Hillary Mutyambai, ya ce ba tare da wani bata lokaci ba, za a fara aikin kama mutanen masu lasisin mallakar bindigar da suka ki bin dokokin, su sama da dubu hudu, a karbe bindigar, sannan kuma a tuhume su.

A watan Fabrairu ne gwamnatin kasar ta Kenya ta bayar da umarnin tsaurara dokokin mallakar bindiga a kasar.

Sai dai kuma daga cikin kusan mutane dubu 14, da ke da rijistar mallakar bindiga a Kasar, kusan dubu tara ne kawai suka gabatar da kansu domin sake duba cancantar su rike bindigar, zuwa wa'adin lokacin da aka bayar na watan da ya wuce.

Karin mako daya ma da aka yi bayan wa'adin kusan bai tsinana komai ba, domin karin wadanda aka samu sun gabatar da kansu ba su da wani yawa.

Hakan ne dai kusan a ce ya harzuka shugaban rundunar 'yan sandan kasar, inda ya bayar da umarnin kama dukkanin wadanda ba su gabatar da kansu ba.

Shugaban 'yan sandan na Kenya ya ce karuwar aikata laifukan da ke da nasaba da bindiga da ake gani a kasar, ya sa dole a tilasta bin wannan doka.

Ya umarci kwamandojin 'yan sanda na yankunan kasar da su fara kama duk masu lasisin mallakar bindigar da ba su gabatar da kansu ba, kuma su kwace bindigar, sannan kuma su gurfanar da su a gaban kotu.

Wani sabon bincike da aka yi na yawan wadanda suke rike da bindugogi a Kenya ya nuna akwai kananan bindigogi da dogaye 750,000 a hannun mutane a kasar, wanda hakan ya fi yawan gaba dayan bindugogin da ke hannun'yansanda da sojojin kasar.

Karkashin matakin raba mutane da bundugogin ne musamman wadanda suka mallake su ba bisa ka'ida ba, gwamnati ta bayar da wa'adin kwana 90 domin fara gurfanar da masu bundugogin ba lasis, domin karfafawa 'yan kasar guiwa su mika makaman da ke hannunsu.