Hotunan Afrika daga 28 Yuni - 4 Yuli 2019: 'Yan kwallo, masunta da manoma masu cike da fushi

Wasu hotuna da aka zabo daga sassa daban-daban na nahiyar Afirka a wannan mako:

Philemon Otieno da Sadio Mane Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A ranar Litinin ne dan wasan kasar Kenya, Philomeno Philemon Otieno ya zarta Sadio Mane na Senegal a wasa a gasar cin kofin nahiyar Afirka duk da cewar Senegal din ta yi nasara a wasan da aka tashi 3-0.
Yaro ya kama kifi daga ruwa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A ranar Laraba ne wani yaro ya cika hannunsa fal da kifi sadin a lokacin bikin shekara na tuna wa da Ranar Kaura ta Kifi a fadin Afirka ta Kudu.
Yanayi ne da ake kama kifi a duk shekara Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption ...Bikin dai na jan hankalin al'ummar Durban zuwa bakin ruwa kuma idan suka je suna kokarin ganin sun kama kifi.
'Yan sandan na Isra'ila sun kama jama'a da dama Hakkin mallakar hoto AHMAD GHARABLI
Image caption A ranar Litinin 'yan sandan a birnin Tel Aviv na Israila suke kokawa da wata mai zanga-zangar nuna rashin amince wa da wariyar launin fata da Yahudawa 'yan asalin Ethiopia suke zargin jami'an tsaron da shi, bayan wani dan sanda da ba ya aiki ya harbe wani matashi dan asalin Ethiopia.
Masu zanga-zangar dai magoya bayan madugun adawa ne Martin Fayulu. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A ranar Lahadi ne masu adawa a kasar Kongo suke bayyana ra'ayoyinsu yayin wani maci da aka gudanar a ranar bikin murnar samun 'yancin kasar.On Sunday Congolese opposition a birnin Kinshasa.
Mai zanga-zangar ya lullube fuskarsa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Har wa yau, a ranar ta Lahadi an kuma samun barkewar zanga-zanga a birnin Omdurman na Sudan, inda wani mai zanga-zanga ya yi kira ga sojoji da su bar mulki...
Suna son sojoji su bar mulki Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption ... ba shi kadai ba ne akwai daruruwansa.
Mnaoma ma sun shiga zanga-zangar
Image caption A ranar Juma'a ma wasu masu sana'ar auduga da zaren ulu a kasar Afirka ta Kudu sun yi zanga-zanga a birnin Lethoso domin nuna rashin amincewa da kamfanin kasar China da cewa ba a biyan su kudaden kayan da akae saya daga wurinsu.
Mafi yawancin mutanen da ke wurin 'yan cirani ne Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hoton wasu mazauna birnin Tripoli na Libya ke nan a ranar Laraba, bayan asarar da suka yi sakamakon wani harin sama da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 44 a wani wurin tsaren mutane da ke wajen birnin, in ji wani jami'in UN.
'Yan sanda na dauke da makarar dan uwan nasu domin sa shi a kabari Hakkin mallakar hoto Empics
Image caption A ranar Juma'a ne 'yan sanda kasar Tunisia suka yi ban kwana da abokin aikinsu wanda aka kashe a wani harin kunar bakin wake a kusa da 'yan sandan sintiri a birnin Tunis.

AFP da Getty Images da Nur Photo da kuma Anadolu Agency ne suka samar da hotuna

Labarai masu alaka