'Yadda bilicin ya lalata min jiki daf da aurena'

An Indian woman receives a facial at a beauty salon in New Delhi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Matan Indiya da dama suna yin bilicin

Cikin murya mai ban tausayi Shiroma Pereira (ba sunanta na gaskiya ba) ta ce "Ban yi kyau ba sam ranar aurena. Na fi muni a ranar fiye da kowacce.

Tana zaune ne a kusa da Colombo, babban birnin Sri Lanka. Kamar dai sauran mata Kudancin Asiya, ta yanke shawarar fara bilicin ne shekara guda kafin aurenta, don ta kara kyau da sheki.

Ta shaida wa sashen BBC Sinhala cewa: "Wata biyu kafin auren na je shagon gyaran gashi na mata suka ba ni wani mai da zan yi amfani da shi don ya sa ni fari.

"Bayan da na yi amfani da man na tsawon mako guda sai fuskata ta yi fari tas. So na yi na dan yi haske kadan amma a karshe sai fatata ce ta kone."

Dabbare-dabbare a jiki

A maimakon matashiyar mai shekara 31 ta mayar da hankali wajen shirin bikinta da gayyatar bakin da za su je, sai ga shi duk ta kashe kudadenta a wajen magance illar da man bilicin ya yi mata.

Image caption Shiroma Pereira ta sha fama da illar da bilicin ta jawo mata - inda ya bar mata tabo a jikinta da bayan wuyanta

"Wasu kuraje suka feso min a jiki sannan jikin duk ya yi dabbare-dabbare."

Man bilicin din da aka ba ta a shagon gyaran gashin ba ya cikin mayukan da hukumomi suka yarda a yi amfani da su a Sri Lanka. An shigar da shi kasar ne ba bisa ka'ida ba ta kasuwar bayan fage.

Ana iya ganin dabbare-dabbare a wuyan Pereira har bayan da ta kammala magance matsalar.

A yanzu dai hukumomi a Sri Lanka suna yaki da sayar da mayukan bilicin a kasar sakamakon yawan samun korafe-korafen illarsu.

Kasuwa

Amma wannan matsala ba a Sri Lanka kawai ta tsaya ba. Miliyoyin mutane mafi yawa mata a yankin Asiya da Afirka suna daukar tsauraran matakai don su koma farare.

An kiyasta cewa kamfanonin da ke yin mayukan bilicin a duniya suna da jumullar kudi dala biliyan 4.8 a shekarar 2017, kuma an yi hasashen cewa hakan zai nunka sau biyu zuwa dala biliyan 8.9 a shekarar 2027.

Yawanci 'yan Asiya da Afirka ne suka fi bukatar mayukan.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An yi hasashen cewa kudin da kasuwar mayukan bilicin ke samu zai kai dala biliyan 8.9 a shekarar 2027

Kayan bilicin sun hada da sabulai da mayuka da kwayoyin magani har da ma allurai da aka tsara don su sanya sinadarin melanin ya dinga fita a hankali, kuma sanannu ne sosai.

A cewar Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO, duk mata hudu daga cikin 10 a Afirka na amfani da mayukan bilicin.

A Afrika, Najeriya ce kan gaba inda kashi 77% na matan kasar ke amfani da mayukan bilicin. Sai Togo da ta zama ta biyu da kashi 59% sannan Afirka Ta Kudu mai kashi 35%.

A Asiya kuwa Indiya ce kan gaba inda kashi 61% na matan kasar ke bilicin, sai China mai kashi 40%.

Kalubale na karuwa

Karuwar bukatar kayayyakin bilicin ya sa kalubalen na karuwa.

A bara hukumomi a Ghana sun yi gargadi masu ciki kan shan magungunan bilicin da ke dauke da sinadaran glutathione.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kayayyakin bilicin sun hada da mayuka da sabulai da magungunan hadiya da allurai

Mata a kasar na shan maganin ne da fatan 'ya'yan da za su haifa su zama farare tun daga ciki.

Afirka Ta Kudu tana da tsauraran matakai kan hana amfani da kayayyakin bilicin.

Gambiya da Ivory Coast da kuma Rwanda a farkon shekarar nan duk sun haramta amfani da kayayyakin bilicin da suke dauke da sinadarin hydroquinone, wanda ke rage samuwar da melanin, amma kuma zai iya jawo lalacewar jiki na din-din-din.

Melanin wani sindari ne mai launin ruwan kasa da baki wanda ke bai wa fata kala.

Yin magani

Cibiyar Kula da Lafiyar Fata ta Birtaniya ta ce, "ana iya amfani da kayayyakin da ke dauke da sinadarin hydroquinone ba tare da sun yi wata illa ba karkashin kulawar babban likitan fata don magance wuraren da ya yi dabbare-dabbare a jiki kuma ya yi aiki."

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mafi yawan 'yan Congo na amfani da mayukan bilicin masu dauke da sinadarin hydroquinone

Cibiyar ta kuma ce wasu kayayyakin bilicin din suna da amfani a bangaren lafiya.

"Wasu mayukan bilicin din suna iya taimakawa, amma dole sai idan likitan fata ne ya ba da izinin amfani da su kuma karkashin kulawarsa, idan ba haka ba suna iya yin illa," a cewar Anton Alexandroff, mai magana da yawun cibiyar.

Biyan bukata

Ammam cibiyar ta jadda cewa "babu wata sahihiyar hanya da likitoci suka yi amanna da ita da ta mayar da dukkan jiki fari."

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sinadaran da ake hada mayukan da su na jawo wa jiki mummunar illa

"Babu wata hujja da ke nuna cewa mayukan da ake saya barkatai na iya taimakawa. Za a iya samun biyan bukata. Za su kuma iya mayar da jikin fari ko kima ma ya fi da baki, kuma fata za ta rasa muhimman abubuwan da suke taimaka mata," kamar yadda Alexandroff ya yi gargadi.

Amma likitoci kan bayar da umarnin amfani da wasu kayayyakin bilicin don warkar cututtuka kamar cutar fata ta melasma.

Wata cutar fata ce da manya ke yi inda jikin ke yi dabbare-dabbaren ruwan kasa ko fari, kuma yawanci a fuska.

Mata sun fi fama da ita, musamman idan suna da ciki.

"Likitan fata na iya ba da ire-iren mayukan bilicin da hukumomi suka yarda da su don magance cutar," a cewar Alexandroff.


Illar su

Aama yawanci mata sun fara saye da amfani da kayayyakin bilicin ba tare da izinin likitoci ba, amma kuma suna iya yi musu mummunar illa kamar:

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Fesowar kuraje da kuma kumburin fata

Kwaile fata da radadi

Kaikayi da tashin fata

(Bayanai - Hukumar Lafiya Ta Birtaniya NHS)


Sinadarin Mercury

Wasu kayayyakin da ake bilicin da su na dauke da sinadarai masu illa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu bincike sun gano cewa mayukan bilicin masu dauke da sinadarin Mercury na da illa ga lafiya

WHO ta ce "Mayukan bilicin masu dauke da sinadarin Mercury na da illa ga lafiya."

Sannan ta kuma gano "kayayyakin da ke dauke ds sindarin mercury ana yin su ne a China da Dominican Republic da Lebanon da Mexico da Pakistan da Philippines da Thailand da kuma Amurka".

Kayayyakin na dauke da sinadarai masu cutarwa kamar yadda sinadarin mercury ke rage samuwar sinadarin melanin.

Kungiyar Tarayyar Turai da wasu kasashen Afirka sun haranta amfani da mayukan jiki da ke dauke da sinadarai masu illa.

Amurka da Canada da Philippines wasu tsirarun kasashen sun bayar da damar sanya mercury kadan.


Lafiya

"Mercury guba ne," a cewar Alexandroff, kuma zai iya jawo matsalolin da suka shafi lafiya.

Babbar illar mercury da ke cikin mayuka da sabulan bilicin su ne:

Hakkin mallakar hoto Getty Images
  • Lalata koda
  • Kurajen jiki da bata kalar fata da kuma tabo
  • Bata karfin fata wajen kare jiki daga kamuwa da cututtuka
  • Farga da damuwa

(Bayanai: WHO)


Tunanin mutane

"Mutane na dauka cewar dukkan mayukan fata ba su da illa. Mutane da dama ba sa tunanin barzanar hakan ga lafiya. Dole mu damu da wannan halayyar," in ji wani likitan fata a Amurka Shuai Xu.

"Ko yaushe ina mamaki idan marasa lafiyar da ke zuwa wajena suka nuna min mayuka daban-daban da suka saya ba tare da izinin likita ba."

Yana koyarwa a Makaranta Likitanci ta Feinberg ya kuma yi bincike a kan illar da mayukan shafawa ke da su.

Wasu mayukan na dauke da sinadaran steroids da ka iya illata mara lafiya in dai ba likita ne ya bayar da shawara ba.

Illa

Dr Xu yana kokarin ganin an sanya tsaurarn matakai don daina samar da kayayyaki masu illa.

"Ba a sa wa kasuwar samar da kayan shafa ido kamar yadda ake yi wa ta magunguna.

"Manyan masana'antu na kaucewa amfani da kayayyaki masu illa, amma muna da matsaloli da yawa ta bangaren shigo da kayan shafe-shafe."

Kasuwar cike take da kayayyaki marasa inganci wadanda da wahala a gane su. Yana yi wa manyan masana'antu matukar wahala su hana kungiyoyin da suke samar da jabun kayayyakin.

Dr Xu ya ce wasu kayayyakin ma ba a rubuta sinadaran da aka yi amfani da su a jiki.

"Ba ka san wa yake samar da su ba. Kuma ba za ka iya mayarwa masu sayarwa ba."

Ya yi gargadi mutane da su kauracewa irin wadannan kayayyakin su nemi mafita.

"Gaba daya dai a iya ce dukkan kayayyakin ba su da illa. Amma idan za ku sayi mayukan bilicin masu karfi sosai a intanet to fa dole sai kun kula."

Fafutuka

Ana zargin masana'antar fina-finai ta duniya da nuna bambancin kalar jiki, abin da ke sa miliyoyin mata rashin yarda da kansu.

Hakkin mallakar hoto Suruthi Periyasamy
Image caption Kungiyoyi da dama sun kaddamar da kamfe domin magance wannan matsala

Kungiyoyi da dama sun kaddamar da kamfe domin magance wannan matsala.

"Baki kala ce mai kyau" na daya daga cikin kamfe din da aka kaddamar don karfafawa matan indiya gwiwa don su kaucewa mayukan bilicin.

Wadanda suka shirya gangamin Pakistani equivalent UnFair & Lovely sun yi amfani da wani sako da ke cewa "Ba sai kina fara ne za ki kasance kyakkyawa ba".

Shirin Beautywell Project na Amurka kuwa an kaddamar da shi ne domin hana al'ummar 'yan ci ranin Somaliya amfani da kayan bilicin.

Abar bauta

Suruthi Periyasamy 'yar yankin Tamil Nadu ta kudancin Indiya ne.

Shekara biyu da suka gabata matashiyar mai shekara 24 ta dauki hoto ta hanyar kwaikwayon wata abar bauta Lakshmi (abar bautar da mabiya addinin Hindu suka yi amannar tana azurta mutum) a wata fafutuka mai taken 'Dark is divine'.

Ma'anar kamfe din ita ce don a nuna cewa ko abar bautar ma ana siffantata a matsayin baka ce.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An fi sa fararen mata a fina-finai

Labarai masu alaka