Senator Abbo: An gurfanar da sanatan da ya doki mace a gaban kotu

Sanata Abbo Hakkin mallakar hoto Senator Abbo

Babbar Majistare da ke Zuba a Abuja ta amince da bayar da belin Sanata Elisha Abbo a kan kudi naira miliyan biyar, 'yan awanni bayan da 'yan sanda suka gurfanar da shi bisa tuhume-tuhume guda biyu na cin zarafi.

Kotun ta kuma ce dole ne sanatan ya mika sunan mutum biyu da za su tsaya masa.

Shi dai sanata Abbo ya ki amince wa da laifuka biyun da ake tuhumar sa da su.

Sanata Abbo dai ya bayyana ne a wani bidiyo yana dukan wata mai tsaron shagon kayan jima'i.

Sanata Elisha Abbo ya shaida wa BBC cewa shi ne a cikin bidiyon da aka yi ta bzawa amma kuma ya ce an goge bangaren da matar ita ma take bugun sa.

Kwamishinan 'yan sandan birnin Abuja, Bala Ciroma ya shaida wa BBC cewa an gurfanar da sanatan amma kuma bai fadi abubuwan da ake tuhumar sanatan da su ba.

Jaridar Intanet ta Premium Times, wadda ta fara sakin bidiyon, ta rawaito mai magana da yawun 'yan sanda, Anjuguri Manzah, cewa "'yan sanda sun shigar da shari'a ne bayan sun ga irin halayyar sanatan a bidiyon".

A ranar Larabar da ta gabata ne sanata Abbo ya yi kuka tare da neman afuwa kan abin da ya aikata, a wani taron manema labarai, kwana guda bayan da 'yan sanda suka ce sun fara bincike.

An samu wasu rahotanni da ke nuna an tsare sanatan a ranar Alhamis, amma an bayar da belinsa washe gari Juma'a.

Dan takarar shugabancin Najeriya na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya tofa albarkacin bakinsa a kan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan bidiyon nan da ya karade shafukan sada zumunta wanda ke nuna yadda sanata Abbo ya make matar.

Alhaji Atiku Abubakar ya ce ya yi wa sanatan farin sani amma kamata ya yi matasan shugabanni irinsa su zama abin koyi.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Atiku ya kara da cewa ya kamata sanatan ya mika kansa ga 'yan sanda.

"Ina shawartarsa da ya fito fili ya nemi afuwa sannan ya mika kansa ga 'yan sanda domin ya nuna dattako," Atiku ya fada.

A wani sakon daban kuma, ya ce ya kamata jam'iyyar PDP ta dauki matakin ladaftarwa a kan sanatan.

"Ina kira ga uwar jam'iyyarmu ta PDP da ta dauki matakin ladaftarwa a kansa, su ma 'yan sanda su tabbatar cewa doka ta yi aikinta."

Sanata Elisha Abbo dai yana wakiltar mazabar Adamawa ta Arewa ne a majalisar dattawa, kuma wannnan shi ne karon farko da ya je majalisar.

Sanatan mai shekara 41 yana cikin 'yan majalisar dattawa mafi kankantar shekaru a majalisar.