'Littafin Bible zai kara tsada'

Getty Images Hakkin mallakar hoto Getty Images

Masu wallafa litattafan addinin Kirista a Amurka sun yi gargadin cewa sabon harajin da Amurka ke kokarin saka wa kan kayayyakin China zai sa kudin litattafan Baibul ya karu.

Sun bayyana cewa harajin zai sa su daina wallafa wasu bugun na Baibul din.

Yunkurin Shugaba Trump na kara kashi 25 cikin 100 na haraji kan kayayyakin China zai shafi kayayyakin Chinar na kusan dala biliyan 300 wadanda litattafan addini na ciki.

China ce kan gaba a duniya wajen buga littafin Baibul.

Tuni dama wasu kungiyoyin addinin Kiristan suka ce ba lallai su iya ci gaba da raba littafin bible kyauta ba saboda tsadar da zai yi.

Ana dai samun takun saka tsakanin Amurka da Chinar musamman kan harkokin kasuwanci.

Ko a kwanakin baya ma sai dai Amurkar ta yi barazana ga kamfanin waya na Huawei inda ma'aikatar kasuwancin kasar ta dakatar da huldar kasuwanci da haramta wa kamfanin sayan kayan kasar bisa dalilan da suka shafi tsaron kasa.

Labarai masu alaka