Trump ya raba gari da jakadan Birtaniya

Donald Trump Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Trump ya ce Amurka ba ta kaunar jakadan, Sir Kim Darroch, kuma ba zai sake aiki da shi ba

Shugaba Donald Trump ya caccaki gwamnatin Birtaniya da jakadanta a Amurka a matsayin martani na wasu bayanan sirri da jakadan ya yi a kan shugaban na Amurka wadanda aka yi satar fitar da su.

Kalaman batancin dai sun sa dangantakar da ke tsakanin gwamnatocin kasashen biyu ta dan yi tsami a 'ayn kwanakin nan.

A wasu jerin sakonnin Tweeter da Trump din ya yi, ya ce daga yanzu ba zai kara wata mu'amulla da jakadan na Birtaniya ba, Sir Kim Darroch.

Shugaban ya bayyana hakan ne 'yan sa'o'i bayan da Firaministar Birtaniyar Theresa May, ta yaba da jakadan, da cewa har yanzu tana da cikakken kwarin guiwa da yarda a kansa;

Jakadan na Birtaniya a Amurka ya caccaki gwamnatin Shugaba Trump inda ya bayyana ta da cewa, ta bankaura ce, mai rauni kuma wadda ba ta dace ba.

Hakkin mallakar hoto PA Media
Image caption A takardun sirrin, Sir Kim Darroch ya ce gwamnatin Trump ta bankaura ce kawai

A takardar diflomasiyya ta sirri wadda aka yi satar fitar da ita wadda Sir Kim Darroch, ya rubuta a ciki ya ce fadar gwamnatin Amurka, karkashin Trump ta sukurkuce tare da rarrabuwa.

Jakadan ya kuma bayyana gwamnatin ta Trump da cewa, ta bankaura ce, mai rauni kuma wadda ba ta dace ba.

Kan wadannan kalamai ne a yanzu shugaban na Amurka ya mayar da martani, tare da nuna rashin jin dadinsa ta Twitter, inda ya bayyana cewa yana fatan ganin an yi sauyi, a sama, wato dai sun raba gari da jakadan, yana neman da a janye shi daga Washington.

Ya ce shi bai ma san wannan jakada ba, kuma ko ma ya yake, ba a sonsa a Amurka, Ya kara da cewa a sakon nasa na Twitter, ''ba za mu sake yin wata harka da shi ba.''

Shugaban ya kuma ce, Theresa May ta yi shirme a shirin Birtaniya na ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai, sai dai ya ce, babban abin jin dadin shi ne, nan ba da jimawa ba, Birtaniya za ta samu sabon Firaminista.

Tun da farko kafin martanin na Trump, Mrs May da kuma ma'aikatar harkokin wajen Birtaniyar sun bayyana kwarin guiwarsu a kan jakadan, amma kuma sun nesanta kansu daga ra'ayinsa.

Sir Kim dai ya yi zama na arziki da gwamnatin ta Trump, sannan kuma ya yi aiki tukuru na ganin cewa an samu nasarar ziyarar baya-bayan nan ta shugaban na Amurka a Birtaniya.

A wani sakon na Tweeter Mista Trump ya ce ya ji dadin wannan ziyara ainun, amma ya ce Sarauniya ce ta fi burge shi.