Lesley Nneka Arimah ta lashe kyautar Caine Prize

Lesley Nneka Arimah Hakkin mallakar hoto Caine Prize
Image caption Arimah tana zaune a Amurka ne kuma tana aiki a kan wani littafin yanzu haka

'Yar Najeriya Lesley Nneka Arimah ta lashe wata babbar kyauta da labarin da ta rubuta wanda 'yan mata ke rayuwa tsirara haihuwar uwarsu har sai sun yi aure.

An ba ta kyautar dala $12,500 (kimanin naira miliyan 4.5) bayan da ta lashe kyautar Caine Prize a gasar marubutan Afirka ta takaitattun labarai.

Arimah ta shaida wa BBC cewa sakon da take son isarwa shi ne bambancin kallon da al'umma ke yi wa mata masu aure da kuma 'yan mata.

Alkalan gasar sun ce "wannan wani salo ne na bayyana gwagwarmayar da mata ke yi na samun daidaito".

"Labarin Skinned ya canza alkiblar abin da aka saba ji kullum, inda ya kalubalanci al'adu sannan kuma ya shimfida sabuwar hanya ga matan duniya," in ji Peter Kimani wanda shi ne shugaban kwamitin alkalan.

Ya kara da cewa: "Ta yi amfani da jimloli masu ratsa jiki, inda aka bayyana wata duniya mai cike da rudani inda kuma babu wani salihin bawa, sannan kuma aka sadar da masu karatu da wata sabuwar rayuwa."

Labarin Skinned ya haska rayuwar Ejem, wadda ta fito daga wata al'umma inda 'yan mata suke fita tsirara daga wasu shekaru har sai sun samu miji.

Arimah wadda haifaffiyar Birtaniya ce kuma girman Najeriya, ta ce ta samu kwarin gwiwa ne daga wata hira da ta yi wata kawarta kan yadda aure a Najeriya "ke bai wa matan aure dama su gane kanuwansu."

"Mace ce mai wuyar sha'ani, shi ne iyayenta suka ce mata lallai sai ta canza hali domin ta samu mijin aure," Arimah ta cewa kawar tata, "bayan ta yi auren ne kuma rayuwarta ta daidaita".

An kirkiri kyautar Caine Prize a shekarar 2000 wadda ake bayar da ita ga wani marubuci dan Afirka kan kananan labarai da aka rubuta a harshen Ingilishi.

Labarai masu alaka