Gwamnatoci sun gaza wajen bai wa yara ilimi

Al

Hukumar Raya Ilmi da Kimiyya da kuma Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO, ta yi gargadin cewa kasashen duniya suna gazawa wajen sauke nauyin bai wa yara ilmi.

A wani muhimmin rahoto da ta fitar a ranar Talata, Unesco ta ce bisa alkawarin da kasashen duniya suka yi karkashin sabbin Muradun cigaba Masu Dorewa, wato SDGs, ya kamata dukkan yara su kasance suna zuwa makaranta a kalla firamare nan da shekara ta 2030.

Rahoton ya ce muddin ba a matsa kaimi a wasu kasashen a Afirka ba, kasa da rabin yaran ne za su kammala karatun firamare izuwa lokacin, bare ma a yi batun karatun sakandare.

Najeriya ce take da yawan yara wadanda ba sa zuwa makaranta, kamar yadda wani rahoto na hukumar bunkasa ilimi da al'adu na Majalisar Dinkin Duniya, Unesco ya bayyana.

Rahoton ya yi kiyasin cewa a kalla yara miliyan 10 wadanda yawacinsu mata ne ba sa zuwa makaranta.

Duk da cewa kasar tana da dokoki da suka tilastawa bai wa yara ilimi kyauta, akwai miliyoyin yara da suke barace-barace a tituna ko kuma kananan sana'o'i.

Ilimin firamare kyauta ne a Najeriya, amma iyaye suna fakaicewa rashin kudin mota da kayan makaranta da kuma kayan karatu a matsayin dalilan da suke hana su kai 'ya'yansu makaranta.

Gwamnatin ta ce batun ciyar da dalibai - wanda aka kaddamar a shekarar 2016 wanda yake amfanar da yara miliyan 10 yana sa su zuwa makaranta.

Duk da cewa wannan shirin yana fuskantar zarge-zargen cin hanci ga wasu jami'an gwamnati musamman a jihohi, wata matsala da hukumomi suka ce suna bakin kokarinsu wajen magance matsalsar.

Hukumar Unesco ta ce duniya ba za ta iya cimma muradun ci gaba mai dorewa na Majalisar dinkin Duniya game da bai wa yara ilimin firamare nan da shekarar 2030.

Karanta wasu karin labarai

Labarai masu alaka