2023: Shin Tinubu na sansana kujerar shugaban kasa?

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bola Tinubu ya ce ba da yawunsa kungiyoyi suke tallansa ba

Jagoran jam'iyya mai mulki ta kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi watsi da wani yunkurin wasu kungiyoyi na tallata shi a matsayin mai sansana kujerar a 2023.

Mista Bola Tinubu ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter, inda ya ce ba shi da alaka da kungiya mai suna "Asiwaju Reloaded Ambassadors' Nigeria'.

Ita dai wannan kungiya ta buga hotunan Tinubun ne a huluna hana-sallah da riguna da ke dauke da rubutu "Tinubu 2023."

Sanarwar ta ce "Muna ta ganin hotuna a huluna da riguna da ma takardu da ke dauke da Bola Tinubu 2023 da aka ce wata kungiyar da ba mu san ta ba da ake kira 'Asiwaju Reloaded Ambassadors' Nigeria'.

Ya ci gaba da cewa "Asiwaju Bola Tinubu bai da masaniya kan kungiyar da kayayyakin kamfe da take rabawa."

Daga karshe sanarwar ta ce, "A saboda haka, ta wannan kafar, ba da yawunmu wannan kungiyar take abin da take yi ba kuma mun barranta kanmu daga dukkanin aikace-aikacenta"

Wane ne Tinubu?

Ku san za a iya cewa babu wani dan siyasa mai wanda Allah ya ara wa rana a siyasance a Najeriya kamar Ahmed Bola Tinubu, kasancewar sa mutum daya tilo da galibin siyasar wani yanki take hannunsa.

Ahmed Bola wanda tsohon gwamnan jihar Legas ne ya raini mutane da dama da yanzu haka su ke da bakin fada a yankin kudu maso yammaci.

Shi ne mutum na farko wanda ba gwamna ba da ya ce ba ya son gwamna mai ci ya nemi tazarce kuma jam'iyya ta ba shi hadin kai.

Jagaban, kamar yadda ake yi masa take, yana da yara irin na siyasa a zangon mulkin Buhari na farko, inda da dama daga cikin ministoci da sauran nade-naden gwamnati da aka yi wa 'yan kudu maso yammaci suka kasance 'yan gidansa.

A yanzu haka akwai masu ganin shugaban majalisar dattawan kasar da na wakilai duka 'yan bangaren Bola Ahmed Tinubu ne.

Ana yawan kwatanta karfin siyasar Jagaban a yankin kudu mao yammaci da marigayi MKO Abiola, wani wanda shi ma ya rike siyasar yankin na wani lokaci mai tsawo.

Babu rami me zai kawo rami?Sharhi, Usman Minjibir

Bisa al'ada da kuma faruwar abubuwa a al'amauran yau da kullum musamman a siyasa, a kan samu kungiyoyi da daidaikuwar mutanen da ke tallar mutum domin a zabe shi tun ma lokaci bai yi ba.

Wani lokaci wanda ake yi domin sa kwata-kwata ba shi da masaniya, amma mafi yawancin lokaci ana yi ne da masaniyar mutumin.

To amma saboda yanayin siyasa sai mutumin ya yi alaye ya ce ba shi da masaniya.

Bisa la'akari da irin tsadar buga hotunan dan siyasa a abubuwa kamar hula ko atamfa ko sabulu da dai sauransu, zai wuya wata kungiya ko kuma mutum haka kawai ba a sa shi ba ya rinka tallan wani dan takaran da daga baya zai yi Alla-wadai da shi.

A kan samu irin wannan yanayi a duk lokacin da sabuwar gwamnati ta hau, inda mutumin da ke sha'awar gadar wannan kujera zai iya daukar nauyin wasu mutane ko kungiyoyi su fara yi wa mai rike da kujerar da ma sauran al'ummar kasa hannunka mai sanda.

Akwai tazara sosai daga yanzu, kasa da wata biyu da hawan sabuwar gwamnati zuwa 2023 lokacin da wa'adin Shugaba Muhammadu Buhari zai kare.

Abin zuba ido a gani dai yanzu shi ne ko Bola Ahmed Tinubu zai amince da irin wadannan kungiyoyi masu yi masa fatan alkairi da za su yi ta fitowa a nan gaba.

Labarai masu alaka