Yadda manyan jami'an gwamnati ke lalata da mata a Afghanistan

Wata mata
Image caption Wannan tsohuwar ma'aikaciyar gwamnati ce kuma ta ce wani babban minista ya yi yunkurin tilasta mata yin jima'i

Kasar Afghanistan ta dade cikin zargin lalata da mata musamman manyan jami'an gwamnati. Duk da cewa jami'an sun musanta, BBC ta ji daga matan da abin ya shafa.

A wani gida da ke karkashin duwatsun da suka kewaye birnin Kabul, na hadu da wata tsohuwar ma'aikaciyar gwamnati. Ta bukaci da kar a bayyana sunanta amma kuma tana so duniya ta san labarinta.

Ta ce wani tsohon uban gidanta, wanda babban minista ne ya sha tsangwamar ta sannan kuma wata rana da ta shiga ofishinsa ya yi kokarin cin zararfinta.

"Kai-tsaye ya tambaye ni ko zan kwanta da shi domin a yi min alfarma. Na ce masa ni kwararriya ce kuma na cancanci aikin.

"Ban taba zaton za ka fada min haka ba. na mike zan tafi sai ya rike hannuna kuma ya janyo ni zuwa wani daki a bayan ofis dinsa.

"Ya tura ni cikin dakin sannan ya ce min kar ki damu abin ba zai dauki lokaci ba, mu shiga.

"Na bugi kirjinsa na ce masa dakata, kar ka sa na yi maka ihu. Wannan shi ne ganin karshe da na yi masa. Raina ya yi matukar baci."

Ko ta kai rahoton abin da ya faru?

"A'a, ajiye aikin na yi saboda ban aminta da gwamnati ba. Idan kuma ka je kotu ko wurin 'yan sanda za ka ga yadda suke karbar cin hanci. Babu wani wuri da zaka kai kuka cikin sauki, in kuma ka yi magana sai a ce mata ne masu laifi," in ji ta.

Tsohuwar ma'aikaciyar ta ce wasu matan guda biyu sun ba ta labarin cewa ministan ya yi masu fyade - zargin da BBC ba ta iya tantance sahihancinsa ba.

Ta ce: "Yana aikata hakan ne ba tare da wani dar ba saboda babban kusa ne shi a gwamnati."

Kasar Afghanistan tana cikin kasashe masu hadari ga mata. Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya na 2018 ya bayyana yadda ake tilasta wa matan da aka yi wa fyade da su janye korafin da suka shigar.

A mafi yawan lokaci ma ana zarginsu ne da laifi kan abin da aka aikata ma su. Korafi kan abin da manyan mutane suke aikatawa ba abu ne mai sauki ba a wannan yankin.

Wannan dalilin ne ya sa akasarin matan da muka yi magana da su guda shida ba su yarda mu ambace su ba.

Amma daga tattaunawar da muka yi da su mun fahimci cewa barazanar fyade da mata ke fuskanta matsala ce babba wadda ta karade duka ma'aikatun gwamnati sannan ta shafi kowa da kowa.

'Abin ya zama jiki yanzu'

Na hadu da wata mata da take son ta bayyana labarinta ita ma a wani ofishi kusa da wani wajen shakatawa.

Ta nemi aiki a gwamnati amma ba ta samu ba sai da aka umarce ta da ta hadu da wani mataimaki na musamman ga Shugaban Kasa Ashraf Ghani.

"Mutumin yana yawan fitowa a hoto tare da shugaban kasa. Ya nemi da in zo ofishinsa na musamman. Ya ce min zo ki zauna, zan sa a dauke ki. Ya matso kusa da ni ya ce mu sha giya mu kwanta," ta bayyana.

Image caption Ofishin Shugaba Ashraf Ghani ya musanta cewa "jami'an gwamnati da 'yan siyasa suna yada karuwanci"

"Zabi biyu gare ni a lokacin; ko dai na karbi aikin ko kuma na fice. Idan na karba ba a kansa matsalar za ta tsaya ba, wasu mutanen da dama za su nemi su kwanta da ni.

"Abin ya girgiza ni sosai kuma na ji tsoro na yi tafiyata kawai."

To ya batun aikin, na tambaye ta. Ta ce ta yi kokarin kiran ma'aikatar a kan hakan sai suka fada mata cewa: "Ai kamar a turo maki da kudi ta asusunki na banki ne amma sai kika ki dauka."

Kuka ta fara yi muna tsaka da tattaunawa, ta ce: "Wadannan suke hana ni barci, su saka ka fushi da ciwon damuwa."

"Idan ka kai korafi wurin alkali ko 'yan sanda su ma sai su nemi su yi nemi su kwanta da kai. Saboda haka wurin wa mutum zai kai kuka kenan?

"Abin ya zama kamar al'ada yanzu ta yadda kowanne namiji ma so yake ya kwanta da ke."

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Afghanistan tana cikin kasashen da rayuwa take da kunci ga mata

A kan yi shuru game da irin wadannan labarai ko kuma a tattana su cikin rada har sai a watan Mayu, lokacin da Janar Habibullah Ahmadzai ya zama dan adawar siyasa.

Janar Habibullah dai tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara ne. Ya yi magana a kan batun ne yayin wata hira a wani gidan talabijin din kasar.

Ya zargi manyan jami'an gwamnati da kuma 'yan siyasa da "yada alfasha".

Ofishin shugaban ya ki yarda yi yi magana da manema labarai sannan kuma bai bayar da amsar tambayoyin da aka tura masa ta imel ba.

Sun ce mu duba wani tsohon bayani da suka fitar cewa dukkanin kalaman Janar Ahmadzai ba gaskiya ba ne.

Nargis Nehan minista ce a gwamnatin kasar kuma ta wallafa a shafinta na Twitter cewa:

"A matsayina ta minista a gwamnatin jam'iyyar National Unity Government (NUG), ina tabbatar wa mutane cewa wadannan zarge-zargen ba gaskiya ba ne."

Sai dai shahararriyar mai kare hakkin mata Fawzia Koofi - kafin daga baya ta zama 'yar majalisa - ta ce ta samu korafe-korafen cin zarafi daga mata wadanda jami'an gwamnati ke yi masu.

"Martanin gwamnati shi na kare kai. Sun dauki abin kamar wata adawa ce ta siyasa ba abin da ya shafi matan Afghanistan," in ji ta.

"Ana yawan aikata rashin gaskiya. Mazan da suke aikatawa suna jin cewa babu mai taba su a gwamnati shi yasa suke kara aikata laifukan."

Image caption An zabi Fawzia Koofi a matsayin 'yar majalisa ne a shekarar 2005

Gwamnati ta yi umarni da a binciki zargin cin zarafin. Ofishin babban lauyan gwamnati ne wanda shugaban kasa ya nada yake gudanar da binciken.

Na hadu da mai magana da yawun babban lauyan gwamnatin Jamshid Rasooli a ofishinsa na birnin Kabul. Hoton Shugaba Ghani yana rataye a bayan teburinsa.

Na tambaye shi cewa me yasa mutane ke zargin cewa binciken da suke gudanarwa ba mai adalci ba ne? Sai ya ce:

"Kundin tsarin mulki ya bai wa babban lauyan gwamnati damar cin gashin kansa. Sannan kuma mun nemi masu kare hakki da 'yan gwagwarmya da su shigo cikin binciken domin mu tabbatar wa da mutane cewa za mu yi adalci."

Na fada masa cewa matan da muka yi magana da su sun ce ba su aminta da hukumomin gwamnati ba saboda haka ba za su iya kai korafi ba.

"Mun yanke shawarar cewa ba za a bayyana wadanda suka kawo korafi ba," in ji shi. "Wadanda suka bayar da hadin kai za mu kare su da iyalansu daga barazana."

Dimokuradiyya ta zo wa Afghanistan ne a wani yanayi da ya lakume rayukan dubban mutane.

Wani bangare na yakin da aka yi shi ne na tabbatar wa da mata 'yanci wadanda aka rika cin zarafi a karkashin mulkin Taliban.

Jagoran shirin kungiyar Nato na Resolute Support a kasar bai yarda ya yi magana kan batun ba, inda ya ce wannan matsalar cikin gida ce.

An sha tura wa hukumar MDD ta mata bukatar su yi magana amma babu amsa. Ofishin jakadancin Birtaniya ma a kasar ya ki cewa komai.

Wani lokaci mai hadarin gaske ga mata a Afghanistan. Sun daura damarar damawa da su a tataunawar zaman lafiya da ake yi tsakanin Taliban da Amurka.

A wasu wurare a fadin kasar mata da dama sun samu sa'ida tun bayan da aka hambarar da gwamnatin Taliban a shekarar 2001.

Sai dai wannan ci gaban da aka samu ba zai yi wani tasiri ba idan ba a hukunta masu aikata cin zarafin ba.

"Ina son shugaban kasa ya sani cewa hakkinsa ne ya saurari koke-koken mata. Idan hakan zai taimaka wajen zaunar da kasa lafiya to ya kamata ya dauki mataki," in ji daya daga cikin matan da suka yi magana da mu.

"Wata rana gaskiyar lamarin za ta bayyana amma abin ba nan kusa ba ne."


Labarai masu alaka