Sniper: NAFDAC za ta hana sayar da maganin kwari 'mai illa' a Najeriya

Professor Mojisola Christianah Adeyeye Hakkin mallakar hoto NAFDAC
Image caption NAFDAC ce Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Maginguna ta Najeriya

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Maginguna ta Najeriya NAFDAC ta sanar da hana sayar da wani maganin kashe kwari "mai illa" daga kasuwanni da shaguna a fadin kasar.

NAFDAC ta sanar da hakan ne a ranar Alhamis inda ta kara da cewa haramcin zai hada da yi da kuma shigo da duk magani mai dauke da sinadarin Dichlorvos cikin kasar.

Haramcin na baya-bayan nan ya shafi Sniper da sauran magungunan da ake yi wa shuka feshi da suka hada da Tankill da Gladiator Liquid da Executor Liquid da Smash Super Liquid da DD Force da Glovan da Philopest da Wonder Liquid da Rid-Off da NOPEST da kuma SUMODDVP.

Hukumar ta ce ta sanya haramcin ne saboda yadda ake amfani da magungunan ba bisa ka'ida ba da kuma yadda suke jawo cutar sankara da cutar matsalar numfashi ga wasu mutanen.

Hakkin mallakar hoto Twitter/@NafdacAgency
Image caption Mojisola Adeyeye, ta ce sun bai wa masu hada magungunan da masu sayar da shi wata biyu su kawar da su daga kasuwanni

Da take jawabi a wani taron manema labari shugabar NAFDAC Farfesa Mojisola Adeyeye, ta ce sun bai wa masu hada magungunan da masu sayar da shi wata biyu su kawar da su daga kasuwanni daga yanzu zuwa 31 ga watan Agustan 2019.

NAFDAC ta kara da cewa dole mutanen da ke amfani da su a gonaki da shuka su nemi izini daga hukumar kafin su shogo da magungunan Najeriya don amfani.

Ta ja kunnen mutane masu amfani da shi a gidaje don kashe kwari cewa su daina don maganin na da matukar illa.

NAFDAC ta ce ta damu kwarai da ganin 'yan Najeriya na cikin walwala sannan kuma su dinga duba abin da ke jikin robar maganin don sanin me suke amfani da shi.