Shi'a: 'Yan Shi'a na zanga-zanga a fadin Najeriya

rikicin shi'a

'Yan kungiyar Shi'a sun shiga kwana na uku suna zanga-zanga a Abuja, amma a ranar Alhamis lamarin ya bazu har zuwa Legas da Kaduna.

Mabiyan kungiyar wacce ke samun goyon bayan kasar Iran zanga-zangar mai taken "ba za mu yarda ba" a birnin Legas don neman a sako musu jagoransu Sheik Ibrahim Elzakzaky, wanda har yanzu yake tsare a hannun hukumomin Najeriya.

An samu cunkoson ababen hawa a Abuja a hanyoyin da masu zanga-zangar suka bi, yayin da mutane da yawa suka dinga neman tserewa don gudun fadawa rikici.

Wasu kuwa a shafukan sada zumunta sun yi ta wallafa sakonni na shawartar mutane cewa kada su bi hanyar Dandalin Eagle Square.

Masu zanga-zangar sun so zuwa Dandalin Eagle Square ne amma sai 'yan sanda kwantar da tarzoma suka hana su karasawa.

Sun yi dogon layi suna maci daga Dandalin Unity Fountain zuwa Eagle Square kuda babbar sakatariyar gwamnatin tarayya, inda a nan ne 'yan sanda suka tare hanya don hana su ci gaba da tafiya.

'Yan sanda sun kama wasu shugabanninsu kuma an yi artabu sosai yayin da jami'an tsaron suka dinga harba musu hayaki mai sa hawaye. Mutane da dama sun jikkata.

Bayan da aka yi rikici da 'yan shi'ar da jami'an tsaro ranar Talata a Abuja, sai shugaban 'yan sanda na kasa M.A Adamu ya bayar da umarnin yin sintiri a babban birnin kasar da kewaye.

'YAn shi'ar suna irin wannan zanga-zangar a Kaduna kuma a ranar Alhamis din, inda can ma jami'an tsraon suka tare hanyoyi don hana su ci gaba.

Dukkan kwamishinonin 'yan sandan da ke jihohin da ke makwabtaka da Abuja na cikin shirin ko-ta-kwana da tabbatar da tsaro da doka a jihohin.

Hakkin mallakar hoto Kola Sulaimon
Hakkin mallakar hoto Kola Sulaimon

Labarai masu alaka