Mutum 11 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Nijar

Shugaban Nijar Hakkin mallakar hoto Getty Images

A kalla mutum 11 ne suka rasa rayukansu wasu bakwai kuma suka bata a wani hadari na jirgin kwale-kwale a gulbin Tibirin Gobir kusa da garin Maradi.

Wani jirgin ruwa ne dauke da mutane kusan 40 ya nutse yayin da suke neman ketara gulbin daga gaba daya zuwa daya gabar.

Gwamnan jihar Maradi Zakari Umaro ya ce "A yanzu an tsamo mutum 14 amma uku ba su mutu ba, sannan ana ci gaba da sauran mutane a cikin ruwan.

"Da wuya mu san yawan wadanda ruwa ya tafi da su, sai dai iyalansu sun zo suna dubawa don tantancewa".

Wani mutum da lamarin ya rutsa da shi ya bayyana yadda lamarin ya faru da kuma yadda ya tsira: "Ni na fidda kaina Allah ya cece ni, ban san dai yadda na tsira ba gaskiya, taimakon Allah ne kawai".

Mai unguwar garin Tibirin ya yi kira ga mutanen da ke anfani da jiragen ruwa da su rika hakuri don gudun sake afkuwa wannan lamari.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun irin wannan hatsari na kifewar jigin kwale-kwale a wannan goulbi na Tibirin Gobir ba.

Labarai masu alaka