Za a yi wani kasaitaccen dambe a birnin Jiddah na Saudiyya

Dib and Khan Hakkin mallakar hoto Super Boxing League
Image caption Billy Dib da Amir Khan za su dambace a ranar Juma'a a birnin Jiddah

Shi dai Amir Khan yana fatan damben da za su yi da abokin hamayyarsa Billy Dib a birnin Jiddah na Saudiyya ya za ma silar da kasar za ta samu daukakar zama babbar cibiyar dambe.

Dan wasan dan Birtaniya mai shekara 32 a duniya zai samu zunzurutun kudi har Fam miliyan bakwai.

Ya yin da abokin hamayyarsa dan Australia shi ke rike da kambun ajin nauyin featherweight, amma ana sa ran zai matsa gaba zuwa ajin welterweight inda za su dambace da Khan.

Khan ya kara da cewa ''Ina ganin karawar da za mu yi da Dib za ta bude wata sabuwar kafa ne da zan nuna a bainar jama'a abin da zan iya yi.''

"Wannan somin tabi ne kan irin shirin da muke yi. Muna son maida kasar Saudiyya ja gaba a fannin wasannin dambe kamar Las Vegas da birnin New York din Amurka, kai har da Landan, kuma na tabbata sannu a hankali za mu cimma manufar.''

'Tauraron Khan ya dusashe'

Damben da za a yi a filin wasa na Sarki Abdallah da ke birnin Jiddah, da farko an tsara shi ne tsakanin Khan da Neeraj Goyat dan kasar India, amma sai aka fasa sakamakon janyewar da Neeraj ya yi saboda raunin da ya ji a hadarin mota.

Shi ma Dib wanda ke rike da kambun ajin Featherweight na duniya daga shekarar 2011 zuwa 2013 ya ce ''Idan ana maganar wanda ya dace mu dambace tare, Khan ya cancanci hakan.''

"Sam ba na son karawa da Keith Thurman ko Shawn Porter, Errol Spence Jr ko kuma Terence Crawford, saboda wadannan mutanen kwararru ne a fagen dambe.

"Kasada kawai zan yi da tarar aradu da ka, saboda babban mutum ne ni kuma dan karami amma duk da hakan zan kokarta.''

Dan dambe Dib dai ya yi nasara a karawa 45 da ya yi, da kuma shan kaye sau biyar, yayin da shi kuma Khan ya yi nasara a karawa 33 da shan kaye biyar.

Labarai masu alaka