Me ya sa batun saka hijabi ya janyo ce-ce-ku-ce a Iran?

Labarin Hijabi a Iran Hakkin mallakar hoto Basij Cyberspace Organisation
Image caption Bidiyon ya nuna yadda aka sauya ra'ayin wata da ba ta da ra'ayin hijabi

A yayin da ake bikin makon hijabi a Iran, wani hoton bidiyo game da muhimmancin hijabin ga mace wanda dakarun juyin-juya-hali na kasar suka amince da shi ya janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta.

A cikin bidiyon an nuna wata matashiya sanye da gyale tare da wani mai shagon sayar da zinari.

Matar wacce ita ce ke bayar da labari a bidiyon, ta ce wanda ke tsaron shagon ya yi ma ta wani kallo na ban sha'awa da kuma murmushi mai jan ra'ayi.

Lokacin da ta tambaye shi game da zinarin da ba na jabu ba, sai ya ce ya kamata ta tafi shagon da ake ajiye zinari a cikin akwati bakwai.

Ya kuma fada mata cewa duk abin da ke da daraja "yana da wahalar samu kuma ya cancanci girmamawa ta musamman," yayin da ya sunkuya ya kalle ta.

Lokacin da wata mace sanye da hijabi ta shigo shagon, sai mutumin ya mike tsaye ya sunkuyar da kai.

Bidiyon ya kare ne inda matar ta farko da ba ta da hijabi ta ce "yanzu na fahimci cewa dole sai na sauya shiga ta, yanzu na gane bambancin zinari na kwarai da kuma jabu."

An kalli bidiyon a Twitter sau 114,000 tun da aka wallafa shi, yayin da kuma aka dinga muhawara kan batun.

Wasu na ganin bidiyon ba zai yi wani tasiri ba wajen yada manufar martabar hijabi, tare da nuna rashin jin dadinsu kan yadda aka danganta mata da zinari: "Mu 'yan Adam ne. An rage mana daraja an kwatanta mu da kayayyaki".

Wasu sun bayyana bidiyon a matsayin bata lokaci da kuma hasarar data.

Dokar Iran dai ta bukaci dole mata su yi shiga irin ta addinin Islama. Wannan kuma na nufin dole mace ta saka hijabi.

Labarai masu alaka