Matar da ta shekara uku da gawar mahaifiyarta a gida a Amurka

Police tape around a tree near a house in the US Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan sanda sun kewaye gidan

An kama wata mata a jihar Texas ta Amurka bayan da aka gano gawar mahaifiyarta a gida mai daki biyu da take zaune ita da 'yarta.

'Yan sanda sun yi amanna cewar marigayiyar mai shkeara 71 ta mutu ne sakamakon faduwa da ta yi a shekarar 2016.

Sun yi zargin cewa 'yarta mai shekara 47 ta gaza taimaka mata sakamakon faduwar da ta yi, abin da ya jawo ta mutu kwanaki kadan bayan faruwar lamarin.

An ga kwarangwal din tsohuwar a tsakar daki. Ita kuma 'yar marigayiyar da tata 'yar, wato jikar marigayiyar suna kwana a daya dakin.

Jikar marigayiyar na da shekara 15 a lokutan da ta rika kwana da gawar kakarta a gida daya.

A sakamakon haka aka tuhumi mahaifiyarta da laifin "illata yarinya" 'yar kasa da shekara 15.

An ajiye yarinyar karkashin kulawar dangi kuma tana karbar tallafi daga hukumar kula da kare yara.

Mahaifiyarta na iya fuskantar zaman gidan yari na tsawon shekara 20 da kuma tarar dala 10,000.

'Yan sanda sun ce marigayiyar mace ce da ake girmamawa a yankinsu, ta yi aiki a wata makaranta tsawon shekara 35.

A yayin da ta yi ritaya kuwa, ta ci gaba da aiki ne a matsayin mai karbar tikiti a yayin wasanni a Seguin.

Labarai masu alaka