Karon 'yan Shi'a da 'yan sanda, Jirgi ya fadi a Nijar

Wasu mata 'yan Shi'a yayin da suke zang-zanga Hakkin mallakar hoto Getty Images

'Yan Najeriya na ciki da wajen kasar sun shaida abubuwa da dama da suka faru ko dai a cikin kasar ko kuma a makwabta a makon da ya gabata.

Ga wasu abubuwa shida da suka faru a Najeriya ko kuma ga 'ya'yanta a wasu kasashen:

1- Karon 'yan Shi'a da 'yan sanda

A ranar Talata mabiya mazahabar Shi'a karkashin jagoranci Sheikh Elzakzaky na kungiyar Islamic Movement of Nigeria suka yi taho-mu-gama da jami'an 'yan sanda, inda 'yan sandan suka ce "an harbi" jami'ansu guda biyu, su kuma 'yan Shi'a suka ce an kashe musu mutum biyu.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Anjuguri Manzah, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce mabiya Shi'ar sun yi kokarin shiga ginin majalisar dokoki ne da karfin tuwo, inda jami'an 'yan sanda suka yi kokarin hana su.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Muryar Muhammad Ibrahim Gamawa

Ya kuma ce sun kama mutum 40 wadanda ake zargi da aikata hakan.

Ita kuwa kungiyar, ta bakin Muhammad Ibrahim Gamawa mai magana da yaunta, cewa take ba ta da makaman da 'yan sandan suka ce 'ya'yanta sun yi harbi da su.

Ya kara da cewa "mutum 100 ne aka kama 'yan kungiyar tasu" ba 40 ba kamar yadda 'yan sanda suka fada.

Za ku iya kallon hotunan barnar da arangamar ta haifar a nan:

2- AFCON 2019: Super Eagles ta kai wasan kusa da karshe

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Chukwueze ne dan wasan da ya fi kowanne kokari a wasan

Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta kai wasan kusa da na karshe a gasar Cin Kofin nahiyar Afirka da ake yi a Masar, bayan da ta doke Afirka ta Kudu 2-1 a ranar Laraba.

Super Eagles ta fara jefa kwallo a minti na 27 ta hannun Samuel Chukwueze, kafin daga bisani Bongani Zungu ya farke a minti na 71. A minti na 89 ne kuma William Ekong ya kara kwallo ta biyu.

Najeriya za ta kara da Aljeriya ranar Lahadi a matakin kusa da karshe wato Semi Finals a birnin Alkahira.

3- Mutum 11 sun mutu a Nijar

Hakkin mallakar hoto Getty Images

A kalla mutum 11 ne suka rasa rayukansu ranar Laraba wasu bakwai kuma suka bata a wani hatsarin jirgin kwale-kwale a gulbin Tibirin Gobir kusa da jihar Maradi.

Wani jirgin ruwa ne dauke da mutane kusan 40 ya nutse yayin da suke neman ketara gulbin daga gaba daya zuwa daya gabar.

Gwamnan jihar Maradi Zakari Umaro ya ce "A yanzu an tsamo mutum 14 amma uku ba su mutu ba, sannan ana ci gaba da neman sauran mutane a cikin ruwan.

4- Buba Galadima ya bayyana a kotu

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Buba Galadima ya bayyana cewa har yanzu fa shi dan jam'iyya mai mulki ne ta APC

Injiniya Buba Galadima, wanda shi ne shugaban tsagin jam'iyyar APC da ake kira rAPC ya bayyana a kotun sauraron korafe-korafen zaben shugaban kasa domin ba da shaida, a ranar Litinin.

A harabar kotun kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Buba Galadima ya ce "'yarsa ta fi kowanne minista a gwamnatin Buhari ilimi da cancanta" bayan da lauyan APC ya tambaye shi ko yana sane da kasancewar 'yar tasa a gwamnatin.

Sannan kuma ya shaida wa BBC cewa har yanzu dan jam'iyyar APC ne kuma "babu wanda ya isa ya kore shi daga jam'iyyar".

5- Mutum biyar da arzikinsu ya fi kasafin kudin Najeriya

Hakkin mallakar hoto YOUTUBE/MO IBRAHIM FAOUNDATION
Image caption Aliko Dangote ne mafi arziki a nahiyar Afirka kuma dan Najeriya ne

Rahoton kungiyar agaji ta Oxform wanda ta fitar a ranar Litinin ya ce akwai mutum biyar a Najeriya wadanda arzikinsu ya yi wa kasafin kudin kasar shal.

Arzikin nasu wanda ya kai dala biliyan 29.9, ya zarce naira tiriliyan 7.29 wanda shi ne kasafin kudin na 2017 - kwatankwacin dala biliyan 23.97.

Jaridar Forbes ta wallafa sunayen mutum biyar 'yan Najeriyar da suka fi arziki a kasar kamar haka:

  • Aliko Dangote
  • Mike Adenuga
  • Abdul Samad Rabiu
  • Folorunsho Alakija
  • Femi Otedola

6- An haramta sayar da Sniper

Hakkin mallakar hoto TWITTER/@NAFDACAGENCY
Image caption An bai wa masu hada magungunan da masu sayar da shi wata biyu su kawar da su daga kasuwanni

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Najeriya NAFDAC, ta sanar da hana sayar da maganin kashe kwari mai suna Sniper daga kasuwanni da shaguna a fadin kasar.

NAFDAC ta sanar da hakan ne a ranar Alhamis inda ta kara da cewa haramcin zai hada da yi da kuma shigo da duk magani mai dauke da sinadarin Dichlorvos cikin kasar.

Haramcin na baya-bayan nan ya shafi Sniper da sauran magungunan da ake yi wa shuka feshi da suka hada da Tankill da Gladiator Liquid da Executor Liquid da Smash Super Liquid da DD Force da Glovan da Philopest da Wonder Liquid da Rid-Off da NOPEST da kuma SUMODDVP.

Wannan dai ya biyo bayan labarin yadda maganin na Sniper ya kashe wata 'yar bautar kasa a jihar Ogun bayan da ta yi amfani da shi a ka domin kashe kwarkwata.

Labarai masu alaka