'Yan sara-suka 500 sun tuba a Bauchi

'yan sanda Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kwamishinan ya ce an bullo da tsarin karbar tubar 'yan sara-sukar ne saboda yawan kama su da kai su kotu ko ajiye su a gidajen yari kawai, ba zai magance matsalar ba

Rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Bauchi ta ce matasa 'yan sara-suka kimanin 500 ne suka suka ajiye makamansu tare da yin watsi da ayyukan na sara-suka, daga watan Mayun 2019 zuwa yanzu.

A ranar Alhamis ne aka yi bikin ajiye makaman a hukumance.

'Yan sara-suka dai kan haddasa hasarar rayuka da jikkata mutane a sassa daban-daban na Najeriya.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Bauchi, CP Habu Sani, ya shaida wa BBC cewa sun bullo da tsarin karbar tubar 'yan sara-sukar ne saboda yawan kama su da kai su kotu ko ajiye su a gidajen yari kawai, ba zai magance matsalar ba saboda kamarinta.

Ku saurari cikakkiyar hirar kwamishinan da Is'haq Khalid ta hanyar latsa alamar lasifikar da ke kasa:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hirar kwamishinan 'yan sandan Bauchi kan sara-suka

Labarai masu alaka