'Yan bindiga sun kashe mutane da dama a wani otal

Al Shabab fighters. File photo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A shekarun baya-bayan nan kungiyar al-Shabab ta kai munanan hare-hare a Somalia

Akalla mutum 12 ne aka kashe a wani hari da aka kai kan wani otal a Kudancin Somalia, kamar yadda jami'ai da kuma wadanda suka tsira suka tabbatar.

Sun ce dan kunar bakin-wake ne ya kutsa kai da mota makare da ababen fashewa cikin otal din Asasey a tashar ruwa ta Kismayo, daga nan kuma sai 'yan bindiga suka shiga cikin ginin.

Shugabannin kabilu da 'yan siyasa ne a cikin otal din.

Cikin wadanda rahotanni suka ce an kashe har da wata fitacciyar 'yar jarida Hodan Naleyeh tare da mijinta.

Daga bisani kungiyar masu fafutuka ta al-Shabab ta yi ikirarin daukar nauyin harin, wanda aka kai ranar Juma'a.

A yanzu jami'an tsaro sun ce sun kawo karshen harin bayan shafe sa'o'i suna bata-kashi da maharan.

An ji karar fashewar wasu abubuwa a cikin otal din jim kadan bayan tashin bam din.

Wani jami'in tsaro a yankin Abdi Dhuhul ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa cikin wadanda aka kashe har da tsohon shugaban karamar hukuma da kuma wani dan majalisa.

Kafafen yada labarai da kungiyar 'yan jarida ta Somalia sun ce Hodan Naleyeh - wacce ke da shaidar zama 'yar kasar Canada da Somalia, wacce ba ta dade da komawa kasar ba tare da mijinta Farid na cikin wadanda aka kashe.

Labarai masu alaka