An ci tarar Facebook dala billiyan biyar

Facebook
Image caption Shafin sada zumunta na Facebook yana da matukar farin jini

Hukumar cinikayya ta Amurka ta ci tarar kamfanin Facebook dala biliyan biyar a matsayin diyya ga binciken da aka gudanar kan bayanan sirrin masu amfani da shi.

Wasu 'yan adawa dai sun bukaci a dauki mataki mai tsauri kan Facebook da kuma shugabansa Mark Zuckerberg.

Wannan za ta iya zama tara mafi girma da hukumar ta sanyawa wani kamfanin fasaha, a yanzu ma'aikatar shari'a ake jira ta amince da hakan kafin a karkare batun.

Duk da cewa babu wani karin bayani da aka fitar akan hakan, wasu na ganin ta yiwu matakan da za a dauka akan Facebook za su kasance masu tsauri.

Yayin da wasu ke da ra'ayin kamata ya yi shi kansa mamallakin shafin Mr Zuckerberg a hukunta shi.

Shugabar cibiyar Dimokuradiyya da Fasaha Nuala O'Connor ta ce tarar ta nuna muhimmancin bayanan sirrin masu amfani da shafin.

Ta kara da cewa an dade ana gargadin kamfanoni su yi kokarin kare bayanan sirrin da suka shafe su, kuma wannan ya hada har da Facebook.

Kawo yanzu dai babban shafin sada zumuntar bai maida martani kan wannan batun ba.

Kididdiga ta nuna a rubu'in farko na wannan shekarar mutum biliyan biyu da miliyan 38 ne sukai amfani da shafin babu kakkautawa a kowanne wata.

Labarai masu alaka