An yi kuka da ni a Zamfara - Yariman Bakura
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

An yi kuka da ni a Zamfara - Yariman Bakura

Latsa alamar lasifika a hoton sama domin sauraren hirar

Tsohon gwamnan Zamfara Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura ya ce rikicin siyasar jihar ya jefa shi cikin tsaka mai wuya.

Jam'iyyar APC ta rasa shugabanci a Zamfara bayan hukuncin kotun koli ya soke kuri'un da jam'iyyar ta samu a dukkanin kujerun da ta lashe a zaben 2019 a jihar, saboda rashin gudanar da sahihin zaben fitar da 'yan takara.

Wasu na ganin Yariman Bakura, gwamnan farar hula na farko a Zamfara daga 1999 zuwa 2007, kuma sanata har zuwa 2019, ya yi tasiri a rikicin wanda ya kai ga APC tashi a tutar babu.

A hirarsa da BBC, tsohon gwamnan, ya ce ya san an yi kuka da shi saboda wasu suna ganin ya goyi bayan wani bangare. Amma ya ce "Na tsaya ne a matsayin Uba"

Sai dai ya ce shi ya ba tsohon Gwamna Abdul'aziz Yari kujerar shi ta Sanata, sannan ya amince masa ya fitar da dan takarar gwamna, lamarin da shi ne musabbabin rikicin.

Tsohon mataimakin Yari, Ibrahim Wakalla, wanda na hannun damar Yarima ne, yana cikin 'yan takara takwas da ake kira G8 da suka raba gari da tsohon Gwamna Yari bayan ya raba kujerun takara ga wadanda yake so a matakin gwamna da na 'yan majalisa da suka kunshi har da 'ya'yan Yarima.

Wasu sun zargi Sanata Yarima da yin fuska biyu, inda aka rasa alkiblarsa.

Amma tsohon gwamnan ya shaida wa Awwal Janyau cewa bai goyi bayan wani bangare ba. "Na yi kokarin yadda za a samu sulhu, domin na tattauna da dukkanin 'yan takarar gaba daya hadi da gwamna amma ba a samu fahimtar juna ba," in ji Yarima.

Ya kara da cewa Allah Ya kai shi matsayin da duk wanda zai tsaya takara walau ya yi siyasa tare da shi ko ya yi jayayya kuma ya dawo, dukkaninsu suna ba shi girmansa.

Ya ce tsohon gwamna Abdu'ziz Yari ne ya nuna ba ya son Wakalla ya gaje shi, shi ne dalilin da ya sa duk yadda yake son Wakkala ya zama gwamna, ba zai yiyu ba.

"Har gobe ina goyon bayan Wakalla, amma gwamna ne ya nuna ba ya son ya gaje shi."

Yarima ya ce yanzu ba ya da karfin da zai ce a yi abin da yake so, saboda mulki ba ya hannunsa. "Na koma mai bayar da shawara," a cewarsa.

Tsarin doki-dora wanda ake ganin ya samo asali daga Yarima shi ne wasu ke ganin ya kai jam'iyyar APC ga rasa shugabanci a Zamfara.

'Har gobe ina nan a Yarima na a Zamfara'

Sanata Yarima ya ce duk da jam'iyyarsa ta rasa mulki amma har yanzu yana da tasiri a siyasar jihar.

"Yarima na yana nan - Yariman nan dai," in ji shi.

Ya ce ko yanzu Gwamnan PDP da kotu ta ba shi mulki tsohon kwamishinansa ne wanda kuma yake ba shawarwari kan abin da ya dace da ci gaban Zamfara.

"Ina nan matsayin uba a Zamfara."

Hakkin mallakar hoto Jihar Zamfara a Najeriya na daya daga cikin jihohi

"Shi kansa gwamnan Zamfara na yanzu Bello Mutawalle ba zai iya yi ba sai da Yarima saboda girman da Allah ya ba ni."

"Duk abin da na bukaci a yi za a saurare ni," a cewar Yarima.

Ya kuma ce saboda alakarsa da gwamnan na PDP, babu mamakin Mutawalle ya sauya ra'ayi ya dawo jam'iyyarsa ta APC.

Matsalar tsaro a Zamfara

Zamfara na daya daga cikin jihohin da suka fi fama da kalubalen tsaro a arewacin Najeriya, musamman matsalolin hare-haren 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane da kuma barayin shanu.

Mutane da dama na alakanta wadannan matsaloli da suka addabi jihar da rashin samun shugabanci na-gari tun bayan komawa mulkin dimokuradiyya.

Kuma Sanata Yarima ya amince cewa talauci ne ya jefa jihar cikin halin da take ciki.

Abin da ya sa Yarima ya daina zuwa Jaje

Tsohon gwamnan ya yi bayani kan abin da ya sa bai damu da zuwa jajantawa mutanen da kashe-kashen da ake yi a jihar ya shafa ba.

Ya ce akwai wasu abubuwan da suka fi zuwa jaje muhimmanci da ya kamata shugabanni su mayar da hankali a kai.

"Na fara zuwa sai na ga abu ne da ake yi kullum, sai na koma ina ba da shawara kan matakan da ya kamata a dauka,"

"Zuwana jaje ba zai kawo karshen matsalar tsaro a jihar ba," in ji Yarima.

Shari'a

Sanata Yariman Bakura ne ya fara kaddamar da Shari'ar Musulunci a Najeriya, inda daga baya wasu jihohi suka yi kokarin kaddamar da tsarin na Shari'a.

Sai dai tun zamanin mulkin Shari'a a Zamfara ake fuskantar rikicin makiyaya da manoma, da satar shanu wadanda ake ganain su ne suka ta'azzara suka koma fashi da makami da satar mutane a yankin arewa maso yammacin kasar.

Wasu na ganin rashin mayar da hankali ga samar da tsari mai dorewa wajen fito da ayyukan da suka shafi ci gaban al'umma, ya yi tasiri ga mawuyacin halin matsalar tsaro da jihar ke fama da shi.

Sai dai tsohon gwamnan ya ce tun lokacin da suka zartar da hukuncin sata kan wasu mutane biyu a zamanin mulkinsa na Shari'a "ba a sake yin sata ba a jihar".

Kuma ya ce lokacinsa ya fito da tsarin da talakawa za su samu walwala ta fannin noma da ilimi da kasuwanci.

"Na yi nawa lokaci kuma na yi iya kokarina, amma wanda ya gaje ni ya zo da na shi tsarin, shi ma wanda ya gaje shi ya zo da na shi salon mulki, haka abubuwa suka sauya".

"An ci nasara a Shari'a tun da babu gidan karuwai a arewa da gidajen caca da na giya," in ji Yarima.

Jama'a da dama dai suna yi wa kallon yunkurin nasa na kafa Shari'a a matsayin wani abu na siyasa, sai dai ya ce irin wadannan mutane ba su san Shari'ar ba ne.

Labarai masu alaka