al-Shabab: 'Yan bindiga sun tarwatsa taron siyasa a Somaliya

Asasey Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A baya dai Kismayo ta kumuta daga rikicin 'yan ta'adda

Akalla mutum 26 ne suka mutu a harin da aka kai na bakin wake a wani otal da ke kudancin Somalia, inda ake kyautata zaton mamatan sun hada da dan ajrida da kuma wasu 'yan kasashen waje.

Wani dan kunar bakin wake ne dai ya kutsa da mota makare da ababan fashewa cikin ginin otal din Asasey da ke Kismayo, kafin daga bisani masu dauke da bindiga suka yi wa ginin tsinke.

Ana kyautata zaton harin ya rutsa da wata 'yar jarida mai aiki a gidan talbiji a kasar, Hodan Nalayeh da mijinta.

Kungiya mai ikrarin Jihadi ta al-Shabab ta dauki alhakin kai harin.

Wani dan siyasa a yankin da wasu 'yan kasar Kenya guda uku da 'yan Tanzania uku da Amurkawa biyu da kuma wani dan Burtaniya na daga cikin wadannan harin ya rutsa da su kuma suka mutu.

Image caption 'Yar Jarida Hodan Naleyah ta yi suna a Somalia

Yadda harin ya faru

An dai kai wannan harin ne lokacin da 'yan siyasa da shugabannin kabilu na yankin na Kudancin kasar ke tsaka da taro a cikin otal din domin tattaunawa kan zaben lardi da za a yi nan gaba.

Wadanda suka shaida yadda al'amarin ya faru sun ce sun ji karar fashewar bama-bamai sannan sun ga 'yan bindiga sun kutsa otal din daga bisani.

An kwashe awowi da dama kafin jami'an tsaro su shawo kan matsalar.

Shugaban Lardin, Ahmed Mohamed ya ce mutum 26 ne suka mutu sannan fiye da 50 sun jikkata da suka hada da maharan guda hudu.