Kisan 'yar shugaban Afenifere na neman raba kan Najeriya

Kayode da Fashoranti Hakkin mallakar hoto Femi Kayode twitter
Image caption Chif Fasoranti ya kasance shugaban kungiyar Afenifere ta Yarabawa

Rahotanni na cewa wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton makiyaya ne suka harbe Funke Olakunrin, mai shekara 58, wadda 'ya ce ga shugaban kungiyar Yarabawa ta Afenifere, Chif Reuben Fasoranti.

An dai ce da misalin karfe biyu na ranar Juma'a ne mutanen suka tsare hanyar Ore zuwa Benin, da ke yankin karamar hukumar Odigbo ta jihar Ondo, inda suka yi garkuwa da mutum bakwai.

Sai dai rahotannin sun ce Funke kawai masu garkuwar da ake zargin makiyaya ne suka kashe a cikin mutanen bakwai da suka yi garkuwa da su.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar ta Ondo inda al'amrin ya faru, Femi Joseph, ya shaida wa BBC cewa babu mutumin da za su kala wa kisan a yanzu haka illa dai kawai su kira su da "'yan bindiga."

Ya kara da cewa Funke ta rasu ne bayan an garzaya da ita zuwa asibiti.

Tuni dai Shugaban Najeriyar, Muhammadu Buhari ya mika alhininsa ga mahaifin marigayiyar, Pa Reuben Fasoranti wanda shi ne shugaban kungiyar Yarabawa ta Afenifere.

Shugaba Buhari ya kuma umarci jami'an tsaro da su gaggauta zakulo mutanen da suka aikata kisan.

Kisan Funke Olakunrin dai ya janyo martani da cece-kuce a kafafen sada zumunta musamman tsakanin kudanci da arewancin kasar dangane da rashin tsaron da kasar take fuskanta.

Tuni dai wasu suka yi ta wallafe-wallafe a shafukan nasu na sada zumunta inda kai tsaye suke danganta kisan marigayiya Funke da Fulani Makiyaya.

Ga abin da wasu ke fadi kan wannan batu a twitter:

Wannan yana cewa kisan da aka yi wa Funke a ruwan sanyi na nuni da irin girman barazanar da matsalar makiyaya ke yi ga gwamnatin Najeriya.

Shi kuma wannan cewa yake yi Fulani makiyaya ne ke fashi a hanyar Ore zuwa Benin tun shekaru uku da suka gabata. Yana mamaki yadda bataliyar sojoji ta 19 ta kasance a kusa da wurin da ake fashin amma ba a dauki mataki ba.

Me kungiyar Afenifere ke cewa?

Tun dai ranar Juma'a ne kungiyar ta Yarabawa ta Afenifere ta fitar da sanarwar kisan da aka yi wa 'yar shugaban kungiyar.

Ba tare da wani nuku-nuku ba, mai magana da yawun kungiyar, Yinka Odumakin, ya dora alhakin kisan a kan Fulani makiyaya.

Yinka Odumakin ya shaida wa jaridar PremiumTimes cewa Fulani ne suka aikata.

Al'ummar yankin kudu maso yammaci na ta tururuwa zuwa gidan Cif Reuben Fashoranti da ke birnin Akure na jihar Ondo domin nuna alhininsu ga rashin da shugaban kungiyar Afeniferen ya yi na 'yarsa.

Afenifere ita ce kungiyar da ke kare kabilar Yarabawa a Najeriya, wadda a bayan-bayan nan an ta jin amonta dangane da batun samar da Ruga da gwamnatin Najeriya ta shelanta yi, kafin daga bisani gwamnatin ta dakatar da shirin.

Labarai masu alaka