Adikon Zamani 13-07-2019
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Adikon Zamani: Me ya sa yawancin matan Hausawa ba su karanta jarida?

Shirin Adikon Zamani na wannan makon ya tattauna ne da Rukayyah Ayuba Adamu mawallafiyar jaridar nan ta kallabi.

Marubuciyar ta bayyana cewa mata da dama ba su cika jin rediyo ko karanta jaridu ba sai dai litattafan soyayya.

Ta kuma ce aikin da tayi na jarida ya sa ta fara tunanin kirkiro kafar da za ta rinka samar da labarai da suka shafi rayuwa a zahiri ba wai soyayya kadai ba.

Za dai ku ji irin dabarun da marubiciyar ke da su da kuma irin gudunmawar da ta bayar wajen jawo hankalin mata domin su fara karatun mujallu da jaridu.

Labarai masu alaka