'Za a tsaurara matakan tsaro a kudancin Najeriya'

IGP Mohammed Adamu Hakkin mallakar hoto Nigeria Police Force

Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya Mohammed Adamu, ya bayar da umarnin kawo sabbin tsare-tsare kan manyan hanyoyin kudancin kasar.

Babban Sufeton 'yan sandan ya ce rundunar ta yi nisa wajen shirye-shiryen kafa shirin "Operation Puff Adder" wanda shiri ne da ake amfani da shi a arewacin Najeriya domin yaki da masu satar shanu da kuma masu garkuwa da mutane da ke sace jama'a kan hanyar musamman Kaduna zuwa Abuja.

Ya ce yanzu wannan shirin zai karade duka manyan hanyoyin da ke kudancin kasar.

An dauki wannan mataki ne bayan da wasu 'yan bindiga suka harbe Funke Olakunrin, mai shekara 58, wadda 'ya ce ga shugaban kungiyar Yarabawa ta Afenifere, Chif Reuben Fasoranti.

Babban Sufeton ya ce wannan yunkuri ne na dakile makamancin wannan mummunan lamari da ya faru da Funke Olakunrin.

Ya kuma yi alkawari ga shugaban kungiyar ta Afenifere cewa za a yi bincike domin gano masu hannu a kisar domin hukunta su.

Sanarwar da mai magana da yawun rundunar 'yan sandar Frank Mba ya fitar ta bayyana cewa, tuni rundunar ta turo jami'anta na tattara bayanan sirri domin neman masu hannu a kisar.

Labarai masu alaka