Birtaniya ta sassauto a kan Iran

Jirgin ruwan dakon mai na Iran Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana zargin katafaren jirgin ruwan na dakon mai zai je Syria ne da man

Birtaniya ta ce mai yiwuwa ta saki katafaren jirgin ruwan dakon man nan na Iran wanda sojojinta na ruwa suka kama, wanda hakan ya haifar da zaman-tankiya tsakanin kasashen biyu.

Sakataren harkokin waje na Birtaniyar, Jeremy Hunt, ya ce ya yi magana da takwaransa na Iran, Javad Zarif domin warware takaddamar, ya yi alkawarin ganin an saki jirgin, idan har Iran din ta bayar tabbacin cewa ba Syria za a kai man ba.

Ba shakka wannan sabon tayi na gwamnatin Birtaniya ka iya sassauta zaman-tankiyar da ake ciki tsakanin kasashen biyu, da kuma a yankin tekun Fasha matuka ainun.

Image caption Jeremy Hunt ya ce Iran tana son a sasanta rikicin jirgin ruwan dakon man

Mista Hunt ya ce, ya jaddada cewa, inda aka nufa da man shi ne abin damuwarsu amma ba wai daga inda man ya fito ba, wato dai yana nesanta Birtaniya daga yunkurin Shugaba Donald Trump, na Amurka na hana Iran fitar da manta zuwa ko'ina.

A baya dai Iran ta musanta cewa Syria za a kai man, amma kuma har yanzu ba ta ce za ta bayar da tabbacin ganin man bai je Syrian ba ko a'a, kamar yadda Birtaniyar ta bukata kafin ta saki jirgin dakon man.

Kama jirgin ya harzuka Iran sosai, wadda daman ta musanta zargin da aka yi mata cewa Syria za ta kai man, har ma ta yi barazanar daukar fansa, lamarin da ya sa aka tsaurara tsaro a jiragen ruwan Birtaniya, da sanya su cikin shirin ko-ta-kwana a tekun na Fasha.

Tun a lokacin da aka kama jirgin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran Abbas Mousavi ya kira matakin kama jirgin ruwan na su a matsayin wani fashin teku, yana mai kiran da a saki jirgin ba tare da bata lokaci ba kuma a bar shi ya ci gaba da tafiyarsa.

Sa'annan Iran ta gayyaci jakadan Birtaniya a Tehran, Robert Macaire, inda ta yi masa korafi a kan abin da ta kira kamawar da ta saba wa doka.

Mita Mousavi ya kara da cewa matakin ya nuna Birtaniya na bin munanan manufofin Amurka, wadanda al'ummar Iran da gwamnatinsu ba za su amince da su ba.

Ko a makon da ya gabata wani jami'in gwamnatin Iran din a yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labaran kasar tasa, IRNA, ya gargadi Birtaniya da ka da ta sake ta shiga sharo ba shanu.

Labarai masu alaka