Za a fara kama bakin haure a Amurka

Wasu 'yan ci-rani daga kan iyakar Mexico Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Karuwar bakin haure da ke son shiga Amurka daga iyakar Mexico ta fusata Shugaba Trump

Dubban mutane ne suka shiga zanga-zanga a birnin Chicago na Amurka, inda suke sukar sabbin tsare-tsaren Shugaba Trump kan shige da fice, yayin da ake fara sumamen kama bakin-haure a Lahadin nan.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar na rike da kwalaye dauke da rubutun da ke cewa: ''Ba yaran da za a killace.'' Wato yaran da su sun zama 'yan kasa amma iyayensu bakin haure ne.

An gudanar da zanga-zangar ne a jajiberin ranar da aka yi niyyar kai sumamen a wasu biranen kasar , domin damke wadanda ake zargin sun shiga kasar ba bisa ka'ida ba.

Matakin kama bakin hauren ya jawo iyalai da dama sun shiga fargaba da tashin hankali, kamar yadda masu mara baya ga bakin suka nuna, yayin da su kuwa 'yan jam'iyyar Democrat suka bayyana matakin da cewa tsabar mugunta ce kawai.

Karuwar da aka gani ta tudadar iyalai daga nahiyar Amurka ta Tsakiya, ta iyakar Mexico, zuwa Amurka ta harzuka Shugaba Trump.

A watan Mayu sama da baki 'yan ci-rani dubu 144 ne aka tsare a kan iyakar kasar da Mexico, wanda hakan ne mafi yawan da aka samu na bakin 'yan ci-rani a cikin wata daya a tsawon shekara 13 a Amurkar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Cibiyar tsare bakin haure ta birnin Tacoma inda 'yan sanda suka harbe wani mutum da ya kai wa jami'ai hari kan kin jinin shirin kama bakin

Hukumomi sun ce wani mutum dauke da makami wanda ya kai hari kan wani jami'in shige da fice a cibiyar tsare 'yan ci-rani ta birnin Tacoma a Amurkar ya mutu bayan da 'yan sanda suka bude masa wuta.

Sansanonin tsare 'yan ci-rani sun cika makil, sannan kuma an yi wa jami'an tsaron kan iyaka yawa, aikin dakatar da kwararar kusan ya fi karfinsu.

Aikin kamen na Lahadi, wanda za a yi a birane tara a fadin kasar, na nufin nuna karfi, kuma kamar yadda Shugaba Trump ya ce, za su kaddamar da aikin fitar da miliyoyin mutane da ya ce sun shiga Amurka ba bisa ka'ida ba.

To amma duk da wannan kururuwa ta shugaban, ana ganin kamen zai mayar da hankali ne kan mutane dubu biyu kawai, wadanda aka riga aka damka musu takardar neman ficewa daga kasar, kuma sumamen kila ba zai wuce na kama mutanen da yawansu akalla bai wuce 200 ba.

Tun da farko Mista Trump ya yi niyyar fara aiwatar da shirin ne a watan da ya wuce, amma ya jingine bisa bukatar 'yan jamiyyar Democrat.

To amma saboda rashin ci-gaba wurin sauya tsarin bayar da mafaka na kasar aka sake dawo da shirin, duk da cewa wadanda za a nufa da shi tuni sun fice daga gidajensu don kada a kama su.